Kwalliyar Sallah
Barkanmu da Sallah tare da fatan ana cikin
koshin lafiya? Allah Ya karbi ibadunmu na alheri Ya kuma maimaita mana wannan
rana. Ina so na janyo hankalin ’yan uwana mata musamman matan aure da su
kasance masu yin ado ga mazajensu, kamar yadda aka yi mana nasiha a lokacin da
muke amare. Don haka a dage wajen amfani da turaren wuta domin tsaftace
muhallinmu da dakunanmu saboda jin dadin iyalanmu.
Ga kadan daga cikin hanyoyin da suka kamata
uwargida ta bi don ganin an samu biyan bukata:
==> Uwargida
ta tabbata ta dage wajen amfani da turaren wuta; a samu kaskon turare a
zuba garwashi sannan a zuba turaren wuta a dora kabbasa a kai sannan a dauki
zanin gado a rufa a don turara shi a duk lokacin da zaa shinfida a kan gado
hade da labule da kuma kayan da za ta sanya a jikinta. Lallai wannan turare na
dadewa sosai a jiki.
==>
Kitso; uwargida ta dage da
yin kitso a kalla sau biyu a wata musamman idan ta kasance mai yawan ‘ya’ya.
Amma an fi so a duk sati maigida ya rika ganin matarsa da sabon kitso. Ta
kasance tana shafa wa gashinta mai don hana fesowar amosanin ka da kuma rage
tsinkewar gashi.
==>
Lalle; jan lalle irin namu
na gargajiya na da kyau sosai. Uwargida ta kasance wajen shafa wannan lalle a
tafin kafarta a kodayaushe domin ban da adon da yake yi yana kuma bayar da
kariya ga lafiyar mace. Idan ba za ta samu damar yin lallen a kodayaushe ba, to
ta kasance tana shafawa a kalla atafukan hannayenta.
==> Dinki; kada uwargida ta ce za ta daina yi wa maigida kwalliya saboda
ta manyanta. Ta dage wajen yin dinki irin na zamani don burge maigida a gida
amma dai kada ta manta da sanya hijabi a duk lokacin da za ta fita zuwa unguwa.
==>
Gyaran fuska; a kwai
wata irin kwalliya wacce ’yan matan yanzu ke yi. Kamar sanya jan baki da gyaran
gira. Sannan ina kira ga mata da su dage wajen yin kwalliya irin ta zamani, ko
da sun manyanta ne, don haka na karfafa soyayya a tsakanin ma’aurata.
==>
Daurin dan kwali; idan
Uwargida tana gida ta kasance mai yin daurin dan kwali irin na zamani don jan
hankalin maigida. Kada ta bari a bar ta a baya ta rika ganin wai ta tsufa. Za
ta iya koyon irin wannan daurin dan kwali daga wajen ’ya’yanta mata ko kuma
’yan uwanta da kuma makwabta. Yana da kyau kowace mace komai tsufanta ta rika
tafiya da zamani.
A yi sallah lafiya.
No comments:
Post a Comment