Shan Ruwa A Matsayin Abu Na Farko Da Safe Na Da Matukan Amfani A Jiki
Muna
Wahalar da kawunan mu musamman a harka da ya shafa lafiyar jikin mu. Akwai wa
su matakai ma su sauki da ya kamata mu dauka domin inganta lafiyar jikin mu.
Daya daga cikin abubuawan nan ma su sauki ya hada da shan ruwa ishashe da safe
kafin mu karya kumallo. Yin hakan ba wanke ciki kawai ya kai ba, yana rage
hadarurruwan cututtuka daban-daban.
Da
farko dai, hakan yana wanke cikin bin-Adama, ya kuma taimaka ma ciki musamman
wajen tantanci ingantattun sunadarin gina jiki yadda ya kamata. Yana kuma daya daga
cikin sirrin abubuawa da ke gyara fata, zaka fatar mutum na sheki domin rowa na
wanke duk wani guba da ke gurbata jini.
Shan
ruwa yana kuma inganta yadda jikin bin-Adama wajen inganta samun karen sabon
jini da jijiyoyi sannan kuma yana taimaka wa wajen rage kiba. Mutun ya tabbata
ka da ya ci wani abu bayan ya sha ruwan da safe sai ya dan jima na dan mintuna
kadan kafin ya nema abinci. Hakan bai kawo wani matsala a jikin bin-Adama, sai
dai ya kara ma mutum lafia da kuzari a jiki.
Yana
da kyau mutum ya sha a kalla moda 4 ( kimanin lita 1) a ranar. Idan yin hakan
mutum yana ganin ya masa yawa, sai ya farawa da kadan kadan, daga baya sai
mutum ya ta kara yawan ruwan ahankali.
No comments:
Post a Comment