A rayuwa, ko ka san inda ka sa gaba kuwa?
Ga masu bibiyar wannan shafi na Duniyan
Fasaha, ina yi maku sallama, kamar yadda muka saba: Assalamu Alaikum. Bayan
haka, a wannan makon kuma, za mu yi ninkaya ne a cikin sabon maudu’i, kamar
yadda muka nuna a sama.
Kafin mu shiga tsokacin namu kai tsaye, mu
fara da wani takaitaccen labari, wanda shi ne zai share mana hanya, domin
fahimtar jigon madu’in namu.
Wani manomi ne da ya mallaki wani kare mai
karsashi da kazar-kazar. Karen nan ba ya zama ko’ina sai bakin titi kuma
halinsa ne a duk lokacin da mota ta zo wucewa a hanyar, sai ya rika bin bayanta
da gudun tsiya da nufin sai ya wuce ta. Haka yake yi a kowane lokaci, tare da
haushi mai karar tsiya.
Kan haka ne sai makwabcin manomin nan ya yi
masa tambaya: “Malam, wai shi karen nan naka, kana ganin akwai ranar da zai iya
cin ma mota a wurin gudu kuwa?”
Jin haka sai manomin nan ya amsa masa da
cewa: “Ni ba ma abin da ke damuna ba ke nan. Ni abin da nake tunani kuma yake
damuna shi ne, idan ma har ya yi nasarar cin mata, to me zai yi kuma? Me zai
samu da zai amfane shi, idan ya kamo motar da yake bi ko kuma idan ya tsere
mata?” Wannan shi ne labarin manomi da karensa da kuma tambayar da makwabcinsa
ya yi masa. Idan mun nazarci labarin nan a tsanake, za mu iya ganin darussa
masu kyau da za mu iya koya a rayuwarmu ta yau da kullum. A rayuwarmu ta yau da
kullum, akwai mutanen da suka yi kama da karen manomin nan, wadanda ke gudanar
da rayuwarsu ba tare da sanin hakikanin inda suka sa gaba ba. Ma’ana, kamar
yadda karen nan yake bin motoci da niyyar sai ya wuce su ko kuma sai ya kamo
su, alhali babu wani abin da zai amfana daga haka, to haka ma wasu mutane ke
yin wasu ayyuka na babu-gaira-babu dalili, ayyukan da ba za su amfane su ba a
rayuwa. Ta haka za ka ga sun dauki wata hanya, wacce ba su ma san dalilin
daukar ta ba, haka kuma ba su san ma inda suka nufa ba a rayuwa. Yin haka kuwa
ba karamar asara ba ce, domin kuwa ga duk mai yin haka, babu abin da zai samu
sai faduwa da asara.
Bari mu sake bibiyar maudu’in nan namu da
misalai na zahiri, domin mu kara fahimtar abin da yake koyar da mu. dauki
misalin dan makaranta, wanda a kullum ake bukatar ya rika zuwa makaranta domin
daukar darasi. Shin me ya kamace shi ya yi? Kamata ya yi ya fahimta da cewa ya
sa gabansa ne wajen neman ilimi. Ilimin da zai samu kuma zai zame masa mai
amfani a duk tsawon rayuwarsa. Idan dalibin nan ya fahimta da cewa lallai ga
inda ya sa gaba, to wannan za ta ba shi damar ya maida hankali ga zuwa
makaranta a kan lokaci, ba fashi. Sannan kuma zai ba da kokari wajen yin karatu
da nazari, domin ya samu nasarar cin jarabawa.
A daya bangaren kuma, idan dalibin nan ya
zabi ya yi koyi da rayuwar karen manomin nan, to sai ya yi watsi da makaranta.
A makwafinta sai ya dauki wani aiki marar tasiri da muhimmanci, ya rika gudanarwa.
Misali, yana iya daukar tadar nan ta kallon kwallon Turawa. Kullum shi ne bata
lokaci wajen kallo, dare da rana. Shi ne karance-karancen labarinsu da kokarin
sanin abin da suke ciki. Za ka ga ya haddace sunayen ’yan kwallo na kungiyoyi
da yawa, ya san yawan kudin da suke samu, ya san kudin da wata kungiya ta zuba,
ta sayi dan wasa kaza, da sauransu. Ta haka dai za ka ga dukkan al’amuransa sun
ta’allaka ga al’amuran wannan kwallo.
Idan zan tambaye ka, a matsayin wannan
matashi na dalibin makaranta, me kallon kwallon Turawa zai tsinana masa? Ashe
wannan aiki da ya tanadar wa kansa bai yi daidai da aikin da karen manomi ya
diba wa kansa na bin mota ba? Yadda karen nan ba zai amfana da komai ba, haka
shi ma dalibin nan ba zai samu komai ba a rayuwarsa. Iyaka abin da zai samu shi
ne, dala miliyan kaza Rooney ke samu, kungiya kaza ta sayi Ronaldo kan dala
miliyan kaza... illa iyaka.
Don haka, kada mu yi koyi da aikin karen
manomi, mu rika yin aikin da zai amfane mu a rayuwa. Mu tabbatar mun san
alkiblar da muka dosa tun kafin mu fara tafiya. Ta haka ne za mu samu nasarar al’amuranmu
na rayuwa, domin kuwa ta haka ne za mu kauce wa abin nan da Hausawa ke kira ‘zuwan
kare a karofi, ba rini ba matsa.’ Allah Ya taimake mu, Ameen.
No comments:
Post a Comment