Hanyoyi 10 da za ki bi wajen rabuwa da kurajen ‘pimples’
Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa daku
cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan
Fasaha.. Na samu sakonni mata da yawa da suka nemi na yi bayanin yadda za su
rabi da kurajen ‘pimples’. Duk da na ta taba gabatar da irin wannan bayanin,
amma sakamakon neman da mutane suka yi na ga dacewar maimaitawa. Ga bayanin
hanyoyin da za ki bi wajen rabuwa da kurajen ‘pimples’:
1 ==>
Da farko ana so awa biyu ko uku kafin ki
kwanta barci sai ki shafa man goge baki wato macline a turanche a fuskarki,
musamman wuraren da kurajen pimples suke da yawa. Ba kowane irin man goge baki
za ki shafa ba, ana so ki shafa farin man goge baki ne. Idan kin ga dama za ki
iya wanke fuskarki idan man goge bakin da kika shafa ya kai minti 30, idan kin
ga dama kuma za ki iya kwantawa da shi har zuwa wayewar gari. Za ki rika
maimata hakan har zuwa wadansu kwanaki, idan kin yi hakan za ki ga canji a
fuskarki.
2
==> Ki kasance mai yawan
shan ruwa. Yana da kyau duk inda za ki je ki sanya ruwa a jikin jakarki ba wai
dole sai kayan kwalliya ba. Yawanta shan ruwa ba wai zai sanya miki laushin fata
ba ne kawai, a’a, zai taimaka miki wajen yaki da kurajen pimples din da suke
fuskarki. Haka yana da kyau ki guji yawan cin abincin gwangwani, kasancewar
suna dauke da wasu sinadarai da za su rika sanya kurajen fuska. Ya kamata ki
yawaita cin ‘ya’yan itatuwa da suka hada da su abarba da lemu da ayaba da
kankana da sauransu.
3
==> Ki rika amfani da
abin shafawar da ake kira ‘Antiodident spray’, irin su Jane Iradale da Neutrogenia
Rapid Clear da Acne Eliminating Spot Gel da sauransu, hakan zai taimaka miki
wajen daidaita man da ke fatarki, wanda masana fata suka ce idan ya yi yawa
yakan haifar da kurajen fuska.
4
==> Ki kasance mai amfani
da man ‘Cornmeal’ a fuskarki, yakan sanya kurajen fuska su motse sannan a
hankali su bace, misali man shi ne, Intagilo Clear Sal Cleanser. Sannan ki rika
amfani da man da ke hana yaduwar kwayar cutar bakteriya, irin wannan man yakan ratsa
kofofin da suke fatar fuskarki da ma jikinki gaba daya, sannan yana yakar
kwayoyin cutar da suke fatarki, a lokaci guda ya daidaita miki yawan man da
yake fitowa daga fatarki. Zai kuma cire miki kwayoyin halittar da suka mutu a
cikin fatarki. Misalinsu; Phytomer Gommage da Luffa-0.
5 ==> Yana da kyau ki ware wata rana ko wadansu
ranaku a cikin mako ba tare da kin shafa kayan kwalliya a fuskarki ba, hakan
zai bai wa fatar fuskarki samun ‘yancin shigar da kuma fitar da iska ta
kofofinta ba tare da wani cikas ba. Haka idan za ki shafa kayan kwalliyar a fuskarki,
to ki yi amfani da kayan kwalliyar da ba sa toshe kofofin fatar fuska.
6
==> Ki kasance mai shafa
mai domin fatar fuskarki ta kasance cikin danshi, kasancewar wadansu kurajen
fuskar sun fi bata fuska idan fuska tana bushe.
7
==> Yi amfani da man ‘Tea
Tree’ domin ba wai kawai yana baje kurajen fuska ba ne, a’a yana rage karfinsu
da kuma kalarsu. Za ki sami ire-iren wadannan man a shagunan sayar da kayan
kwalliya na zamani.
8 ==> Ki kasance mai yin taka tsan-tsan wajen
amfani da ire-iren man shafawar da kike amfani da su a gashin kanki, ma’ana
kada ki sake ya rika taba fuskarki hakan zai iya haifar miki da kurajen fuska,
kasancewar wadansu sinadaran an yi su don su taimaka wa gashin kai ne, don haka
idan suka shiga kofofin fatar fuskarki, sai su haifar miki da matsala.
9
==> Ki kasance mai gasa
kurajen fuskarki: Duk lokacin da kurajen pimples suka fito miki sai ki samu
wani kyalle mai tsafta, sai ki tsoma shi a ruwan zafi, ba wanda ya tafasa ba,
bayan kin tsoma sai ki fito da shi, sai ki rika dora shi a kan wajen da kurajen
suke, sannan ki rika gogawa a hankali, zafin kyallen yakan sa kurajen su motse
daga nan su mutu.
10
==> Ki guje yin amfani da
hannunki wajen fasa kurajen da suke fuskarki, domin hakan yana kara yawansu
hade da sanya fuskarki ta kara cabewa.
No comments:
Post a Comment