Kowa na da lokaci irin nasa yanayin fata. Don
haka a lokacin da wasu za su yi kaujen tafin kafa daban yake da yadda wasu za
su yi na su. Wani a lokacin sanyi yake samun wannan matsalar wani kuma sai zafi
ya shigo yake samun kauje. Don haka dole ne a kula da taffuka kafa. Idan ba’a
kula tafin kafa yadda ta dace ba kafar za ta fara tsagewa ko kuma fashewa. Mata
da dama na mantawa wajen kulawa da kafa a duk sadda suke kwalliya. Me aka yi
idan ko’ina ya yi kyau, amma in aka taka mutum sai a ji kafar da kauje ko kuma
faso. Akwai hanyoyi da dama da za a bi don kulawa da tafukan kafarmu kamar haka;
==> Za a iya amfani da ‘baking soda’ (ana
samunsa a inda ake sayar da kayan hada ket) da man ‘tea tree’ da man lafinta,
sannan a zuba a ruwan dumi a gauraya su, sai a tsoma kafa na mintuna ashirin,
sannan a dirza da dutsen goge kafa. Yin hakan na rage fitowar kauje da faso a
tafin kafa.
==> Man lafinta da ‘sea salt’ da ruwan ‘aloe
bera’ da man ‘rosemary’ a hada su a ruwa, sannan a tsoma kafa na tsawon mintuna
ashirin, sai a dirza kafa har sai kafa ta fita tsaf.
==> Bayan haka, sai a busar da kafa ko a goge da
tawul. Sannan a shafa man ‘glycerin’ da na lafinta a fatar kafa da tafin kafa.
Sai a yanke farce a gyarasu.
==> A samu man ‘glycerin’ da gishirin ‘Epdomr’
(ana samunsu a manyan kantuna da ake sayar da kayan kwalliya) da man ‘tee tree’
da kuma man ‘peppermint’ a zuba su a ruwa sannan a jika kafafun na tsawon
mintuna goma sha biyar zuwa ashirin, sai a dauko dutsen goge kafa a dirdirza. Za
a ga canji.
==> Shafa man kadanya a bayan an wanke kafa da
ruwan dumi, sannan a sanya safa ana kwana da shi. Yin hakan na taimaka wa tafin
kafa sosai.
==> A kasance a kullum ana goge kafar da dutsen
goge kafa, domin samun tafin kafa mai sulbi da laushi.
No comments:
Post a Comment