Abubuwan bukata
·
Dankali
·
Kwai
·
Koren wake
·
Maggi
·
Gishiri
·
Albasa
Yadda
ake Sarrafawa
Da
farko za ki gyara dankalin ki, ki fere ki zuba masa ruwa ki dora a wuta. Ko dai
ki bar shi ya dahu sosai ki daka shi, ko kuma ki dafa shi sama sama ki markada
a Blender ba tare da kin saka ruwa ba. Ki fasa kwai da dan dama ki zuba a ciki Za ki
iya dan barbada fulawa kadan, amma ba dole ba ne Ki goga albasa ko ki yankata
kanana ki zuba, shi ma koren waken ki wanke ki zuba Ki zuba maggi da gishiri
dai-dai misali, sannan ki magutsa su gaba daya Sai ki dora tanda a kan wuta ki
na zuba mai kina soyawa
No comments:
Post a Comment