Yadda za ki lura da hakorinki
Hakora na daya daga cikin abubuwa da ke fitar
da kyawun mace. Don haka ya kamata a ba su kyakkyawar kulawa. Wadansu matan
sukan shiga halin tasku, inda ko an yi abin dariya sai su rufe bakinsu da hannu
kafin su yi dariya, saboda halin da hakoransu suka samu kansu a ciki. A wannan
makon mun taho miki da hanyoyin da za ki yi amfani da su wajen lura da
hakoranki.
Ga abubuwan da ya kamata ki yi da kuma
wadanda za ki gujewa don samun lafiyayyen hakori.
Abin
da za ki yi don samun lafiyayyen hakori
==> Za ki iya amfani da jus din lemon tsami ko
kuma ruwan lemon tsami wajen cire dabbaredabbaren rawaya da ke hakora. Idan
lemon tsami ne sai ki yanka, sannan ki matse ruwan, daga nan sai ki kurbi
ruwan, sannan ki kuskure bakinki. Za ki iya amfani da hannunki wajen cuccudawa.
==> Idan kina so hakoranki su yi fari, kuma abin
sha’awa, sai ki samu ‘ya’yan itacen Strawberries, sai ki yayyanka, daga nan sai
ki yi buroshi da su.
==> Idan kika goge hakoranki da ruwan lemon zaki
ma yana sanya hakora su yi haske.
==> Idan akwai datti ko dabbare-dabbare a
hakoranki, sai ki samu gishiri, ki kuskure bakinki da shi. Ki dangwali gishiri
da yatsanki, sannan ki cuccuda hakoranki.
==> Cin ‘ya’yan itatuwa da alayyahu na cire
dabbare-dabbare a hakori.
==> Ki samu buroshin goge baki, sai ki dangwali
sinadarin hydrogen perodide, sannan ki goge hakoranki da shi.
==> Idan kin ci abinci sai ki goge bakinki,
hakan zai sanya hakoranki su yi kyau da kuma sheki.
Abin da ya kamata ki gujewa;
==> Ki guji yawan shan abubuwan da ke dauke da
sinadarin carbon (Carbonated drinks), wadannan abubuwan shan suna dauke da
sinadarin acid din da ke kashe hakora, sannan ya sanya su samu dabbare-dabbaren
rawaya.
==> Ki guji yawan shan kofi (Coffee) ko
Nescafe,domin suna sanya hakora su yi duhu.
==>
Ki guji yawan cin goro ko shan sigari, domin
suna dauke da sinadarin nicotine da ke kashe hakora da kuma sanya hakora su yi
duhu.
==> Ki guji yawan sha zobo domin yana sanya
hakora su yi duhu.
No comments:
Post a Comment