Shan Lemuna Masu Sikari Na Haifar Da Cutar Rudewa A Lokacin Tsufa
Masana sun gano cewa akwai alaka mai karfi
tsakanin shan lemunan da ke dauke da sikari da cututtukan da suka shafi
kwakwalwa musamman kamar cutar rudewa da cutar mantuwa.
Wadannan cututtukai dai sunfi kama mutane a
lokacin tsufa
A baya dama binciken kimiyya ya alakanta shan
irin wadannan lemuna da cututtuka kamar su ciwon zuciya, rubewar hakori, shanyewar jiki,
kiba da ciwon sikari.
A yan kwanaki da suka shudene aka wallafa
rahotan binciken guda biyu da ke alakanta shan lemuna da cututtukan mantuwa da
rudewa (Alzheimer’s and Dementia) a kundin ilimin likitanci biyu masu suna
‘Medical Stroke Journal’ da ‘Alzheimer’s and Dementia’ Wadanda suka gudanar da
binciken masana ne a jami’ar koyar ilimin likitanci da ke garin Boston a kasar
Amurka.
No comments:
Post a Comment