Yadda za ki yi amfani da fiya da ayaba wajen gyaran jiki
Fiya da ayaba na matukar taimakawa wajen
gyara fatar jiki, sukan sanya fata ta yi sheki da kuma laushi. Kayan hadi:
·
Ayaba
·
Fiya
·
Yogot
·
Man zaitun
Yadda za a
hada:
1==>
Daga farko ki samu ayaba, sai ki bare, ki
yasar da bawon, daga nan sai ki samu fiya, ki bare ta, sai ki zubar da bawon.
Bayan nan sai ki hada ayaba da fiya da kuma kwallon fiyar, sannan ki daka.
2==> Bayan kin gama dakawa, sai ki zuba yogot da
kuma man zaitun. Za ki ci gaba da cakudawa har sai kin tabbata komai ya
gaurayu.
3==>
Daga nan sai ki shafa a fuskarki ko jikinki har na tsawon minti 15.
4==>
Bayan nan, sai ki wanke fuskarki ko sauran jikinki da ruwa mai dumi.
No comments:
Post a Comment