Tare Da Muhammad Abba Gana
{Jikan Marubuta}
A zamanin namu na yanzu mutane da dama suna aiki da blog ne
kawai da manufar samun kudi, ko hanyan samun kudi wasu kuma suna aiki dashi ne
saboda hanya ce da zai taimaka sosai wajen kasuwanci.
Haka kuma ma danfara sukan
samu hanyar danfaran mutane saboda yanda mutane suka sha’afa da aiki dashi. Sau
da dama mutane sukanyi korafin cewa basu samun mutane suna ziyartan shafinsu
wanda sun bi duk wata kayatacciyar hanya daya dace a abi dan ganin mutane
suna da masaniya a kanta.
Abu daya kamata mu sani shine yawan sa ran samun kudi
ta hanyan yanar gizo yana daya daga cikin abubuwan dayake janyo rashin ziyartan
mutane saboda bazaka sa ko kayi abunda ya dace ba kawai matsalar ka kaga dubban
mutane suna ziyar tan shafinka wanda hakan ba karamin abu bane kuma ba abun
gaggawa bane.
Yana da kyau ka kasance na musamman in kana son cimma manufarka
na zama daya daga cikin shahararrun masana kan yanar gizo ko kuma zama daya
daga cikin hamshakan mutane da suke samun kudi ta hanyan yanar gizo.
Maganar
gaskiya, akwai dubban hanyoyi da ake bi wajen ganin shafi ya riske mutane da
dama abu na farko ya kunshi abubuwa masu inganci, duk da cewar ba bangaren nan
zan tabo ba yau zan mayar da hankali ne game da asalin shi shafin wato sarki da
kansa wanda shine “abun dake ciki” ko yaya shafinka ya kasance misali gwani
wajen sura (design) yawan sa a wajen mutane a karshen mako abinda ke cikin
shafinka ne zai sanar da mutane manufanka,
ABU NA FARKO
GWAJIN KWARI (QUALITATIVE
CONTENT)
Kamar
yanda na ambata a baya bazanyi Magana a kan suran shafiba wato design a turace, yanda aka
jera shafi da sauransu, zanyi bayani a kan sarkin shafi shine inganta rubuta
koh abunda ake sawa a ciki wanda shine jijiyan shafinka kuma nasaranka.
Shawara
na anan shine, in kana son shafinka ya dauka ka to dole ka lura ka kuma inganta
wayannan abubuwa dan ganin shafinka ya daukaka wanda zai iya zama ta hanya
daban-daban wanda sun hada da harshe, nahawu, gabatarwa, hotuna da dai makamantansu.
ABU NA BIYU
INGANTA DABI’A (USE CASUAL MANNER)
Wani
abu da zaka ga a sabbin shafuka suna farawane da niyyan samun kudi wanda basu
da masaniya akan yanda ake tafiyar da abun, yaya ake budewa ko kuma yaya za’a
magance idan matsala ta taso wasu daga cikin su kuma sam basu da dabiu masu
kyau wasu sukan bude dan labarai wasu dan wakoki wasu shafukan idan ka gani
kamar inji mai aiki da kansa ne ya bude, yana da kyau in zaka bude shafi ka
zauna kayi nazari a kan shin maisa zan bude??
Ta wani bangaren zan taimaka?
Shin wani yana yin abunda zan yi? Wayannan sune kadan daga cikin abubuwan da ya
kamta ka tambayi kanka kafin bude shafi haka zalika in kazo rubuta abu da zaka
sa a shafinka ya kasance ka rubuta cikin nitsuwa kayi tunanin mai zaka rubuta
yaya kuma zaka rubuta yana da kyau in zaka rubuta abu kayi tunanin kamar tadi
kakeyi da abokinka ko dan uwanka ta hanyan nishadarwa tare da nuna girmamawa a
rubutunka wanda zai sa mutane da dama suyi sha’awar dawowa shafinka.
ABU NA UKU
KADA KA
RUBUTA ABU MAI TSAWO (DON’T POST LONG ARTICLES)
Mutane
da dama suna da ra’ayin kin karanta rubutu masu tsawo a yanar gizo in suna so
su karanta novel sukan ware lokaci na musamman, kayi kokarin zuwa kai tsaye
abunda kake son sanarwa ya zamana a gajarce duk da cewar akwai wasu abubuwa da
bazasu iya gajartuwa ba ko kuma a kankantar dasu in hakan ya kasance ka
rarrabasu zuwa gida-gida wannan ba kawai zai kara mutane masu ziyartan shafinka
ba, mutane da dama zasu ji dadin karanta abu a shafinka saboda basu son
karatanta abu mai tsawo.
ABU NA HUDU
KA YAWAI TA
DUBA HARUFFAN KALMA (ALWAYS CHECK YOUR WRITING SPELLING)
Yana da kyau
kafin ka saka post a blog kabi rubutun da kayi dan duba in da akwai matsala da
yanda nahawu naka ya kasance kafin ka sawa masu karatu ga wayanda suke
aiki da wordpress akwai wani plugin mai suna “after the deadline” wannan plugin
yakan taimaka sosai wajen duba harrufa da kuma jimla da ka rubuta a harshen
turanci amma yana aiki ne da harshe turanci.
ABU NA BIYAR
KA DAGE WAJEN
SAKA SABIN ABUBUWA (TRY AND POST OFTEN)
Mabiyanka wanda
suke son abubuwan da kake rubutawa zasuna marmarin suga kasa abu sabo, in ya
kasance kana sa abu sabo sau guda a wata ko kuma sau daya a cikin sati
uku mabiyanka zasu iya canza shafi izuwa wani wanda a koda yaushe yana sa
sabbin abubuwa, yana da kyau ka ringa sa sabbin abu a kalla sau uku koh biyu a
sati.
Shin
kana da wani hanya wajen ganin blog naka ya zama daya daga cikin shafuka
masana?? zamu so muji ta bakinka dan allah a ajiye a shashin nunaa ra’ayi wato
comment box
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Za'a iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Asslm, muna godiya sossai da sossai.
ReplyDeleteIna da bukatar koyon hada website, inada tambayoyi kuma da dama wadanda za'amin karin haske akansu.
Waalaikumussalam, bismillah ina saura ronka
DeleteAlhamdulillah, Insha Allahu Zan Tuntubeka Ta Facebook Da WhatApp Gabadaya.
DeleteAllah Ya Kara Basira.