Girkin nadadden nama
|
Uwargida barkanmu da warhaka tare da fatan
alheri da kuma fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake
girka nadadden nama. Yana da kyau Uwargida ta kasance mai tsabtace jiki da kuma
iya sarrafa girki dabandaban. Don haka dole ne mace ta dage wajen taka rawar
gani a harkar girki tare da koyon kowane irin salon girki. Nadadden nama dai
ana iya cin sa a kowane lokaci walau da safe ko da rana ko kuma da dare.
Abubuwan da za a bukata:
·
Namar
karamar dabba
·
Man zaitun
·
Garin
tafarnuwa
·
Garin
citta
·
Gurji
·
Garin
masoro (black pepper)
·
Barkono
·
Kori
·
Latus
Hadi:
A samu danyen naman rago wanda bai cika maiko
ba. Sannan a yayyanka da fadi sosai kamar tabarma. Sannan a samu kwano a zuba
garin tafarnuwa a ciki sannan a zuba garin masoro da barkono da garin citta da
kori sannan a zuba man zaitun sai a kwaba ssosai.
A yayyanka gurji salasala a ajiye a gefe. A
samu cokali ana dibar hadin man zaitun ana shafawa a kan naman. A zuba hadin
isasshe sannan a dauko salan gurji ko latus a shimfide shi a kai sannan a yi
masa nadin tabarma. Sai a dauko tsinken sakace hakori ‘toothpick’ a soke naman
da shi yadda nadin ba zai warware ba sannan a saka a na’urar gashi a gasa na
tsawon minti 30 zuwa 35.
No comments:
Post a Comment