Budurci Na: Dalilan Da Ya Sa Mata Da Dama Ba Sa Ganin Jini A Ranar Darensu Na Farko – Ilimin Don ‘Yan Maza Da ‘Yan Mata.
Ba za ka iya kirga adadin aurarrakin da suka
mutu ba sakamakon rashin fitar jini daga gaban amaryar da angonta ya aureta a
matsayin budurwar da shi zai bareta a leda A yadda muka dauka shi ne, sai ango
ya ga amaryar kaca-kaca cikin jini a darensu na farko, shi ne zai tabbatar masa
da cewa amaryar tasa bata taba sanin d’a namiji ba Ita kanta amaryar cike ta ke
da fargaba na ko angon nata zai tono jini ko kuma a’a ko da kuwa ta san ba ta
taba aikata lalata da wani da namiji ba kafin aure. Ba sabon labari bane ba a
wasu zamaninnika da suka gabata cewar har jefa amaryar a ke yi da zarar mijinta
ya yi saduwar farko da ita kuma jini bai fita ta gabanta ba.
Har farin kyalle ake shimfi dawa akan abin
kwanciyar amarya da ango a darensu na farko don a tabbatar da zubar jini daga
gaban amaryar, kuma cikin alfahari za a yi ta yawo da kyallen ana nunawa manya
fa cewa “Wance bata zub da mutuncin taba kafin ta yi aure” Wannan dabi’a ta fitar
jini daga farjin mace a jima’inta na farko ba mu kadai ke da ita ba. Mutanen
Pakistan, Indiya, Bangladesh, Afghanistan da sauran kasashe na da irin wannan tunani
na cewa dole sai jini ya fita daga gaban mace a jima’inta na farko. Kuma idan
har ta sadu da namiji a matsayin saduwar farko, kuma bai ga jini ba, to lalle
ta taba saduwa da wani kafin shi kuma a wancan saduwar tata, jini ya fita Wannan
batu namu ya zo ne da nufin karyata wancan tunani da ke cewa wajibi ne macen da
ba ta taba saduwa da da namiji ba ta fitar jini ta gabanta a yayin saduwarta da
na namiji a karo na farko. Wannan ko kusa ko alama ba gaskiya bane.
Batun shi
ne, ba kowace mace ce ke fitar da jini a lokacin da namiji ya kawar mata da
budurcinta ba, Wasu na fitarwa, wasu kuma basa fitarwa, kuma hakan ba ya na
nufin lalle ba wankakkun ‘yan mata bane don basu fitar ba Domin fahimtar dalilin
da ya sanya wasu mata ke fitar da jini wasu kuma akasin haka a jima’insu na
fari, ya kamata mu fahimci cewa akwai wata fata ko tantani mara kwari da ke
rufe farjin mace tun daga haihuwarta. Fatar ba wai tana rufe kafatanin farjin
mace bane.
Wani abu da ya kamata mu kara fahimta a nan
shi ne, ba dukkanin mace ba ce ke da wannan tattani na budurci a lullube a
gaban farjinta. A yayin da, kamar yadda hoto na sama ya gwada, wasu mata ke
dauke da fatar a lullube da gabansu, wasu ‘yar kadan ce, wasu rabin farjinsu, wasu
kaso biyu bisa uka da dai sauransu. A saboda haka, mace mai tantanin budurci
mai kauri (wanda ya lullube gabanta gaba daya) dole za ta fitar da jini a yayin
jima’inta na farko sakamakon sai namiji ya fasa wannan tantani kafin ya samu
shiga Ita kuma mace mai matsakaicin tantani, dole jinin da zata fitar ba zai
kai na wancan ta farko ba.
Haka abin zai kasance har zuwa kan wacce sam
ba ta da tantanin budurci. Ita wacce ba ta da wannan tantani, ba ta fitar da
jini ko a jima’inta na farko Ga yawancin mata, wannan tantani na fi cewa da
kansa sakamakon yin abubuwa na motsa jiki kamarsu tukin keke, sukuwa a kan doki,
wata ma daga yin rawa ko kuma ta hanyar yin amfani da kyalle a maimakon auduga
a yayin al’ada. Wannan na faruwa ga mace da ke dauke da tantanin budurci marasa
kwari Yana da kyau mu fahimci cewa, tantanin budurci na shafewa da kansa bisa
dalilin girman mace. Anan muna nufin, mace mai karancin shekaru (kamar shekaru
16 ko kasa da haka) na da yiwuwar fitar da jini a jima’i na farko sama da ‘yar
shekaru 25 zuwa sama
Ya kamata maza su fahimci cewa, sau tari ba
ma tsagewar tantanin budurci ke haifar da jinin da mace ke fitarwa a lokacin
jima’inta na farko ba, a’a, wasu mazan kan gaza yin hakuri ne su bi matan a
sannu a hankali ta yadda za su shiga matan har su kai ga yi musu raunin a
gabansu wanda shi ne a lokuta da dama ke haifar da fitar jinni Da a ce maza da
dama na fara yin wasa da mace na tsawon lokaci ta yadda har sai ta kamu ko ta
bukatu, da da dama ba a za ga fitar jini ba a gaban mace ko dai ta hanyar yi
mata rauni ko ta hanyar fasa tantanin budurci A takaice dai, babu wata hanya
takamaimai da mutum zai iya tabbatar da cikar budurcin mace ko akasin haka.
Fitar jini ba hujja ba ce, saboda fitar jini
ya danganta ne ga irin tantanin budurcin da mace ke dauke da shi tun daga
lokacin da aka haifeta. Akalla, kaso 63 na matan duniya ba za su fitar da jini
ba a lokacin jima’insu na farko. Kaso 37 ne bisa hasashe za su fitar da jini a
lokacin jima’insu na farko bisa bincike mai inganci da aka wallafa a wata
mujallar lafiya ta kasar Ingila Samun ilimin budurci na da matukar amfani ga
maza da mata, musamman ma maza. An zargi mata, an wulakantasu, an ci zarafinsu,
aurensu ya mutu, a shekaru da dama da suka gabata ma an jefe mata kawi don ba
su fitar da jini ba a lokacin jima’insu na farko. Wannan ilimi ko shakka babu
zai taimaka wajen kare mutunci da muhibbar mata, tare da fitar da su daga
zargin mazajen aurensu, iyayen da danginsu Mu kiyaye, ba duk wacce bata fitar
da jini a daren farkonta ba ce, wacce ba ta da budurci. Don Allah a yada don
al’umma ta amfana.
No comments:
Post a Comment