Yadda Ake Gyaran fata da kankana
|
Kankana na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwan
dake dauke da sinadaren gyaran jiki da gautsin fata da kuma rage tsufar jiki
domin tana dauke da sinadaren dake wanke maikon dake taruwa a magudanar gumi a
fata wanda yawanshi ke haifar da fesowar kuraje da dama. Don haka, amfani da
kankana a jiki na da matukar mahimmanci sosai ga rayuwarmu ta yau da kullum. A
yau na kawo muku hanyoyi da dama da za’a bi domin yin amfani da kankana domin
samin fata mai laushi da kuma sheki a kodayaushe:
==>
Kodewar fuska: markada
kankana tare da gurji sannan a rika shafawa kamar sau biyu a rana na matukar
magance wannan matsalar. Sannan za’a iya markada kankanar zalla sai a dauko
auduga ana tsomawa ana shafwa a fuska sannan a barshi ya bushe na tsawon
mintuna goma sha biyar. Za’a iya markada kankana da ganyen na’ana’a sannan a
rika shafawa a wannan wajen da fatar ta kode. Amma abu daya nake so a yi amfani
dashi a cikin ababen da na lissafo.
==>
Domin yankwanewar fata: A
markada kankana sannan a zuba mata zuma kadan sai a rika shafawa a inda fatar
ke yankwanewa sau biyu a rana. A samu kankana da ruwan lemun tsami da sukari
sai a hadasu guri daya. Kafin sukarin ta narke sai a rika dirzawa a inda fatar
ta yankwane domin mikar da fatar.
==>
Rage shekaru: A samu
kankana da man zaitun da kindirmo da kuma kwanduwar kwai sannan a kwaba a rika
shafawa a fata a kullum domin samun sakamako mai kyau mai inganci. Za’a iya
markada kankana sannan a samu ayaba a kwaba sannan a hadasu guri daya sai a
rika shafawa a fata. A samu markadaddiyar kankana da madara da kuma fiya sannan
a kwaba a rika shafawa a fata domin samun sakamako mai kyau.
==>
kurajen fuska: a sami
kwallon kankana a busar a rana sannan a daka yayi laushi sannan a tafasa ruwa a
zuba sai a tace sannan a rika wanke fuska dashi.
==>
Gautsin fata: a markada
kankana sannan a zuba mata man ridi da na kwakwa sai a shafa a fata a barshi ya
kai tsawon mintuna ashirin sannan a wanke.
Hello, I enjoy reading through your post. I wanted to write a little comment to support you.
ReplyDeletei really appreciate your great work thanks for drooping your comment
Delete