Yanda zaka boye number ka yayin tura sako (Text Message)
|
Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka barkanmu
da sake saduwa da ku cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye
daga mujallar Duniyan Fasaha, kamar koda yaushe kuna tare ne da Muhammad Abba
Gana, insha Allahu yau zan dan yi bayani ne akan yanda mutum zai boye number
yayin da yake tura sako.
YADDA ZAKA BOYE LAMBARKA A SAKON
Nasha samun sakonin daga gareku ma’abota karatun
wannan shafin cewar shin akwai wata hanya ne da mutum zai bi wajen boye
lambarsa yayin tura sako? Banyi tunani na iya amsa kashi saba’in cikin dari a
sakonin da kuka turo ba bisa wannan tambayar, wanda banji dadin hakan ba shi
yasa na yanke shawarar cewa na rubuta saboda kowa ya amfana.
To a hakikanin gaskiya ba wata kayataccen
lamba wacce wata kamfanin sadarwa dake cikin gida nan Nigeria ta zayyana wanda
zai bada damar boye lamba yayin tura sako kamar dai yanda akan iya boyewa yayin
kiran, hakan kuma baya nuni da cewa duk duniya ba’a iya yi. Wasu kasashe da
suka cigaba sukan yi hakan saboda layukan sadarwansu su basu damar yin hakan. Amma
de a nan cikin gida wato Nigeria akwai wasu daba ru da mutum zayyi wanda shima
zai iya turawa ba tare da wata number ya bayyana ba.
Matakai
1==> Ka shiga Menu na wayanka ka sai ka
zabi ''Message> Setting > Text message > SMS Sending Profile'' Saika latsa ''Option'' ka zabi ''Send
SMS as''saika zabi zuwa ''Email'.
2==> Idan ka zabi ''Sending SMS'' ta
''Email'' saika danna zai tambayeka kasa ''SMS Server'' saika sa lambar layinka
wanda kake son ka boye yayinda kake son tura sako. Saika danna ''Save'' sannan
ka latsa ''Activate''.
3==> Saika koma wurin rubuta sako ka zabi
''Create Message'' saika rubuta sakonka, bayan ka gama saika danna ''Send'',
zasu tambayeka ka rubuta email address, saika rubuta abinda kake so as email
misali: duniyanfasaha@gmail.com ko kuma wani suna da kake bukata.
4==> Idan ka gama saika danna ''Send''
sakon zaije wurin wanda ya karba da cewar daga Duniyanfasaha@gmail.com, sabanin
lambarka, ko kuma wani suna daka sa akan sakon din.
Wannan shine wata hanya wanda mutum zai bi
wajen boye lambarsa yayin tura wa mutum sako.
No comments:
Post a Comment