Hanyoyin kara tsawon gashi cikin sauki
|
Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa da
ku cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan
Fasaha insha Allahu yau zamu tattauna ne a kan hanyoyin da mace zata bi wajen
kara tsahon gashi, Mata da yawa na son ganin gashinsu ya kara tsawo, hakan ba
zai samu ba har sai sun rika kula da gashinsu, kasancewar gashi na kara wa mace
kyau. Akwai hanyoyi da dama wadanda muka kawo miki a yau, idan kika bi su sau
da kafa za su taimaka miki wajen kara wa gashinki tsawo, baki da yalki da kuma
karfi. Wani abu dangane da wadannan hanyoyin shi ne, ba sa bukatar ki kashe
kudi.
·
Daga farko
ki dora man kwakwa a wuta sannan sai ki zuba masa man amla. Daga nan sai ki
gauraya sosai, idan kin tabbata sun gaurayu, sai ki sauke daga wuta, har hadin
ya huce. Sai ki zuba man a kwalba ko murta. Kina shafa wannan hadin a fatar
kanki da gashinki kamar sau uku a sati.
·
Lemun
tsami na sanya tsawon gashi sosai. Ki samu ruwan lemun tsami, sai ki hada shi
da kwai da kuma man amla. Sai ki shafa hadin a fatar kai da kuma gashi. Ki bar
hadin a kanki har tsawon minti 30, sannan ki wanke da ruwan dumi. Za ki iya yin
wannan hadin sau 2 a wata.
·
Ki samu
ruwan Aloe bera, sai ki shafa a fatar kai da kuma gashi, bayan minti 20 sai ki
wanke da ruwan dumi.
·
Man zaitun
na sanya gashi ya yi baki, taushi da kuma tsawo. Za ki iya mayar da man zaitun
ya zama man kitsonki.
Muna so ku san cewa za ku iya zabar daya daga
cikin wadannan hanyoyin, domin kowace hanya za ta biya miki bukata. Idan kuwa
kika yi amfani da gaba dayansu, za su iya sanya a garin gyaran gira ki rasa
ido. A huta lafiya.
No comments:
Post a Comment