Assalamu
alaikum Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku wani
nau’in girki da idan aka yi tabbas za a samu canjin dandano a gida. Shin da
mene ne ake cin farar shinkafa a gidanku? Inji dai ba da miyar dagedage ba ce
kawai? In ko haka ne har yanzu da sauranku a girki, sai a matso kusa a dauki
sabon darasi. Miyar ‘Chicken curry’ dai miya ce ta kasar Indiya wadda ake
hadawa da shinkafa domin kara dadi da gardi da kuma dandano.
Abubuwan da za a bukata
1.
Kaza
2.
Kori
3.
Bata
4.
Nono
5.
Tafarnuwa
6.
Citta
7.
Albasa
8.
Karas
9.
‘Peas’
10.
Koren wake
11. Magi
Hadi
Idan
Uwargida ta wanke naman kaza tsaf kamar yadda muka yi bayani a baya yadda ake
cire karni, sai ta yayyanka kanana sosai yadda za ta raba fatar da kashi sannan
ta ajiye a gefe.
Sai ta
dora tukunyarta mara kama girki (nonstick) sannan ta zuba bata ko man zaitun
isasshe sannan ta zuba naman kazar da ta riga ta yayyanka a ciki ta yi ta
gaurayawa har sai hadin ya fara nuna sannan ta dauko kori mai kyau mai kuma
kanshi ta zuba kamar cokali biyu sai ta ci gaba da gaurayawa.
Sannan ta
dauko albasa kanana ta watsa tare da jajjagen attarugu da tafarnuwa da citta ta
zuba sannan ta debo nono ko madara mara sukari ta zuba a ciki ta ci gaba da
gaurayawa sannan ta zuba magi ta dan rufe na tsawon minti biyu sannan ta sake
budewa.
A wannan
karon za ta zuba yankakken karas da koren wake sannan ta gauraya ta rufe. Bayan
minti daya sai ta zuba ‘Peas’ ta ci gaba da gaurayawa sannan ta sauke. Sai a
zuba a kan farar shinkafa a ci.
No comments:
Post a Comment