Yadda ake yin miyar wake
|
Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan
ana cikin koshin lafiya kamar kullum. A yau na kawo muku yadda ake miyar wake.
Wannan miyar al’adace ta Nufawa kuma suna yawan yin ta a gida ko kuma a taron
bukukuwa da sauransu. Suna kiran miyar da suna ‘Ezowa’ wato miyar wake. Yana da
kyau uwargida ta koyi girke-girke na kabilu dabandaban domin hana maigida cin
abinci a waje, da kuma sanya kunnensa motsi. Anfi hada wannan irin miyar da
tuwon shinkafa.
Abubuwar da za a bukata
1.
Wake
2.
Man ja
3.
Attarugu
4.
Busasshen
kifi
5.
Albasa
6. Gishiri da magi
Hadi
Idan uwargida ta samo wakenta, sai ta jika.
Bayan hakan, sai ta cire kowar jikin waken. Sai ta daura ruwa a wuta. Bayan ya
tafasa, sai ta zuba waken ya yi ta tafasa har sai ya nuna ya yi lugwi. Sannan
sai ta zuba yankakkiyar albasa da dakakken attarugu da manja da busasshen kifi.
Sai a jira miyar ta yi ta tafasa na mintuna kadan, sannan sai a zuba magi da
gishiri. Hhmmn! Lagwada! Ana iya cin wannan miyar ne da tuwon shinkafa. Kuma
anfi son amfani da ita da rana ko da yamma. Lallai idan maigida ya ci wannan
abincin sai kunnensa ya motsa. Da fatan za a girka wa maigida wannan miyar
domin armashi da kuma dandano mai gamsarwa!
No comments:
Post a Comment