INGATTACCEN HADI DON GYARAN NONO
|
Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka barkanmu
da sake saduwa daku cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga
mujallar duniyan fasaha, insha Allahu yau zamuyi bayani ne game da ingantaccen
hadi don gyaran nono.
wannan hadin yana karawa mace girman nono
kuma sam ba ya faduwa. Ko da a ce tana shayarwa ne idan har tana amfani da
wannan hadin sai dai mu ce Allah san barka. Uwargida, ki nemi wadannan
kayayyakin:
1.
Farar
shinkafa
2.
Garin
Alkama
3.
Garin
habbatus sauda
4.
Garin
Ayaba (Plantain).
5.
Gyada mai
malfa (mai zabo)
6.
Aya
7.
Madarar
gari.
8.
Zuma
Za ki bare bayan plantain sai ki yayyan ka
shi, ki shanya ya bushe, sai ki daka, ki hada da garin alkama da garin farar
shinkafa, sai ki hada aya da gyadar ki markada sai ki tace ruwan. Bayan nan,
sai ki dora kan wuta ki zuba garin Plantain da alkama da farar shinkafar da
kika hade a guri daya, sai kuma ki zuba garin madara da zuma, ki dama ya yi
kauri sai ki rika sha safe da yamma. Idan kina shirin yin yaye ne, to ki sha
sati biyu kafin yaye, in kuma ba kya shayarwa, za ki iya sha, sai ki tanadi
rigar mama, wato Brazier mai kyau, wanda zai rika tallafawa mamanki su tsaya
sosai, ki rika sakawa. Ki yi haka na tsawon sati biyu, da yardar Allah za ki
samu biyan bukata. Allah ya tamake mu. Idan kuma baki da halin siyan duka
wadannan kayayyakin da na ambata a baya to kina iya yin kunun alkama ki rika
sha sau biyu a rana, amma za ki rinka sa madarar gari, wato kunun alkama da
madara kenan. Ko kuma ki sami garin hulba, ki tafasa ki rika gasa nonon da shi,
sai kuma ki shafa man hulban a kan nonon zaki ga abin mamaki sannan kuma zaki iya
pasa kwan salwa kina shafawa a kan nonon, sai kuma ki ringa fasa guda uku kina
shan su danye. Insha Allahu za a dace.
No comments:
Post a Comment