Ko kun kasance daga cikin wadanda kurajen
fuska ke bata musu fuska? Shin kun kasance cikin wadanda garin shafeshafen na’ukan
man kara hasken fata, kuraje na fesowa musu tare da barin tabo bakake? Ko kun san
mene ne zai warkar da wadannan tabon da kuma kurajen da sanya fata haske?
Lallai ba wani abu bane illa amfani da lemun tsami na tsawon wata uku ko fiye
da hakan. Lemun tsami na dauke da sinadaren da ke magance kowace irin cutukar
fata, amma idan an yi hakuri. Kasancewar ganin yadda wannan hadehaden lemun
tsami ke taka rawar gani a wajen yaki da cututtukar fata ya sanya a yau na kawo
muku mahimmancin amfani da shi a fata domin samin sauki a wadannan cutukan da
kuma yadda za a yi amfani da su.
==> Amfani
da shi a matsayin man shafawa: a sami man kwakwa sannan a zuba a cikin
murta sai a sami lemun tsami kamar guda daya ko biyu sannan a matse ruwansa a
cikin wannan man kwakwar sannan a kwabasu a rika shafawa a jiki a matsayin man
shafawa. Yin wannan hadin na kare fatar jiki daga cututtuka da dama.
==>
Haskaka gwiwar kafa da gwiwar hannu da kuma yatsar da ta yi baki sakamakon man
kara haske: Idan
gwiwar hannu da gwiwar kaka da kuma yatsun kafa da hannu sun yi baki sosai
sakamakon yawan shafa na’ukan man kara haske. Sai a sami lemun tsami daya a
yanka shi zuwa gida biyu sannan a rika shafawa a inda ya yi baki a jiki na
tsawon minti ashirin safe da yamma a kullum, za a sha mamaki.
==>
kurajen fata: A sami
lemun tsami a yanka shi zuwa gida biyu sannan a rika matse ruwansa ana gogawa a
kan kurajen ko kuma tabon fata. A sannu a hankali tabon zai fara haske har ya
bata. Amma sai an yi hakuri. Ina so idan aka fara amfani da wannan hadin kada a
rika matse kurajen.
==>
Domin cire kwalliyar fuska: Idan
ba a manta ba, a baya na taba fada muku cewa rashin goge kwalliya a fuska
sannan a kwanta bacci na haifar da fesowar kuraje, don haka a sami lemun tsami
sannan a hada da man dogon yaro a sami auduga a rika goge fuskar da hadin har
sai kwalliyar ta fita tsaf kafin a kwanta bacci.
==>
Samin farin hakura: A sami
‘baking soda’ sannan a kwaba shi da ruwan lemun tsami. A dauko magogin hakora
sannan a rika lakutawa ana gogawa a hakora. Yin hakan na sanya hasken hakora
sosai musamman ga masu hakoran da suka riga suka dafe kuma suka canza launi.
==>
Hasken fata: lemun
tsami na dauke da sinadarin bitamin C don haka yawan amfani da shi a fata na
dada hasken fata. Amma ana son amfani da man SPF idan ana yawan amfani da lemun
tsami a jiki ko fuska. Yawan amfani da shi na sanya rana ta rika dakar fuska
amma idan an sami man SPF ana shafawa kafin a fita, hakan na hana rana yi wa
fatar illa.
No comments:
Post a Comment