Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Makulashen Azumi – Kunun Buda Baki Kala 5 Da Yadda Ake Sarrafa Su

Makulashen Azumi – Kunun Buda Baki Kala 5 Da Yadda Ake Sarrafa Su

Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha, Insha Allahu yau zamuyi jawabine akan kunun buda baki kala biyar da yadda ake yinsu. Kunu na daya daga cikin abubuwan da aka fisha a lokacin azumi musammam ma a lokacin bude baki, domin bukatar a dumama ciki a kuma warware kayan hanji. A yau muna tafe da kalolin kunu guda 5 kamar haka;

Kunun Madara

Kayan Hadi
1.      Madarar gari
2.      Danya ko busasshiyar citta
3.      Fulawa
4.      Lemon tsami
5.      Dafafiyar alkama ko shinkafa
6.      Sikari
7.      Masoro mai kwanso

Yadda ake sarrafawa

==> Ki dama madarar gari da ruwa sai ki zuba masoro da citta a ciki sai ki bari ya tafaso.
==> Idan ya tafasa sai ki kawo dafafiyar shinkafa ko alkama ki zuba a cikin madarar ki juya sannan ki kawo fulawa ki kwaba ta da ruwa ki na zuba wa a ciki kina juyawa a hankali har sai ya yi miki kaurin da ki ke so.
==> Sai ki sauke daga kan wuta ki bari ya dan sha iska kadan, sannan ki kawo lemon tsami ki matsa kadan a kai ko kuma iya yadda ya yi miki, sannan ki zuba sikari.

Kunun Gyada

Kayan Hadi
1.    Gyada
2.    Shinkafa
3.    Fulawa
4.    Lemon tsami
5.    Sikari
Yadda ake Sarrafawa

==> Ki jika gyada ta jiku sannan ki wanke ki cire bawon ta. Sai ki nika ki tace ta.
==> Sai ki zuba wannan tataccen ruwan a kan wuta ki zuba danyar shinkafa, amma idan kina sauri za ki iya zuba dafaffiyar shinkafa, ki na juyawa akai-akai saboda ruwan gyadar zai na kumfa yana tasowa.
==> Idan da danyar shinkafa ne sai ki bari har sai shinkafar ta dahu, amma idan da dafaffiyar shinkafa ce sai ki bari har sai kin ji babu gafin gyadar.
==> Ki dama fulawa da ruwa, ki daure kunun da ita. Za ki na zuba fulawar a hankali har sai kin ga kaurin ya yi miki. Sai ki sauke ki matsa lemon tsami idan ya dan huce, sannan ki zuba sikari.

Wannan hanya ce daya kawai da ake yin kunun gyada, akwai wasu hanyoyin daban.

Kunun Mardam

Kayan Hadi

1.    Garin kunu
2.    Citta
3.    Kaninfari
4.    Lemon tsami
5.    Nono
6.    ‘Ya’yan cumin

Yadda Ake Sarrafawa

==> Ki samu ruwa ki zuba a cikin tukunya ki saka citta da ‘ya’yan cumin ki dafa har sai sai kin ji sun fara kanshi.
==> A gefe daya kuma sai ki dama garin kunun, ki zuba nono a kai da dama sannan ki dan kara ruwa kadan, sai ki ringa zubawa a cikin ruwan cittar daya tafasa a hankali, ki rage wuta sosai ki barshi ya yi kamar minti hudu akan wuta.
==> Idan ya yi kauri da yawa kina iya kara ruwa dan kadan.
==> Sai ki sauke, idan ya dan huce sai ki saka lemon tsami. Idan kina so ki na iya saka sikari, ko kuma ki bar shi ki sha haka da gardinsa.

Cumin ana samunsa a wajen masu sayar da kayan kanshi a kasuwa ko kuma a kantinan sayar da kayan masarufi.

Kunun Alkama

Kayan Hadi

1.      Garin alkama da ‘ya’yan alkama
2.      Citta
3.      Kirfa
4.      Sikari
5.      Lemon tsamiKanunfari

Yadda Ake Sarrafawa

==> Ki dafa alkama har sai ta yi laushi sosai.
==> A gefe guda kuma ki dora ruwa a wuta ki saka kanunfari da kirfa a ciki.
==> Sai ki samu garin alkama ki kwaba shi da wani ruwan daban.
==> Ki juye wannan alkamar da kika dafa a cikin ruwan kanunfarin da ke kan wuta, sannan ki
fara zuba kwabin alkamar ita ma a cikin ruwan a hankali.
==> Ki bar shi ya yi kamar minti uku zuwa hudu akan wuta sannan ki sauke.
==> Idan ya huce sai ki zuba lemon tsami da sikari.

Kunun Tsamiya

Kayan Hadi

1.        Garin kunu
2.        Tsamiya
3.        Sikari
4.        Barkono
5.        Kayan kanshi

Yadda Ake Sarrafawa

==> Ki samu gero a sirfa miki sannan a bakace a fitar da dusar. Ki wanke shi sosai ki kuma rege domin gero baya rasa tsakuwa.
==> Sai ki baza shi akan tabarma ya bushe. Idan bushe sai ki zuba barkono da kayan kanshi sannan ki kai a nika.
==> Ki tankade nikan da rariya mai laushi.
==> Ki jika tsamiya, idan ta jiku sai ki tace ki zuba tsamiyar a cikin garin kunun ki kwaba amma ba da kauri ba.
==> Idan kina so kuma kina iya yin gaya, ki zuba ruwa da sikari a cikin garin kunu ki kwaba da kauri.
==> Ki dora ruwa daidai adadin kunun da ki ke so, idan ya tafaso sai ki saka gayan, ki rufe tukunyar har zuwa minti goma don gayan ya dahu.

==> Idan kin tabbatar gayan ya dahu sai ki kawo tafasashshen ruwan ki juye shi a cikin garin kunun da ki ka kwaba, sannan ki juya. Idan ya huce sai ki sa sikari ki sha ko kuma ki sha haka.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *