Gasashen kifi da hadin gurji
|
Assalamu alaikum Uwargida, tare da fatan ana
cikin koshin lafiya. Yana da kyau kowace mace ta rika la’akari da irin abincin
da za ta rika ci domin kulawa da jikinta. Mata da dama sai su dage da cin tuwo
nan ko ba su san cewa ita ana girka shi da hatsi ne, sannan yana dauke da
sinadaren kara jiki, wadanda idan kiba ta yi yawa, takan haifar da cututtuka da
dama. Don haka ne a yau na kawo muku irin abincin da ya dace da uwargida domin rage
kibar. A sha karatu lafiya.
Abubuwan
da za a bukata
·
Kifin
karfasa
·
Kayan
kanshi
·
Magi
·
Albasa
·
Citta da
garin tafarnuwa
·
Gurji
·
Lemun
tsami
·
‘Salad
cream’
Hadi
A samu kifin karfasa sai a wanke shi sannan a
tsane ruwan. Sai a sanya shi a cikin roba mai fadi sannan a farfasa masa magi
da kori da albasa da garin citta da garin tafarnuwa da dakakken barkono da man
gyada kadan, sai a kwabasu waje daya, tare da matsa ruwan lemun tsami kadan. Sannan
a shafa a jikin kifin sai a sanya a gidan sanyi na tsawon awanni biyu, daga nan
a cire shi daga na’ura mai sanyaya kayan abinci.
Bayan haka, sai a dora shi a kan karfen
gashi, wanda ya riga ya yi zafi, a yi ta gasawa, har sai ya gasu sannan a
sauke. A yayyanka gurji kanana, sannan da dafaffen kwai sai a kwaba shi da
‘salad creame’ da dan magi da yaji kadan. Sai a ajiye a kusa da gasashen kifin.
Wannan irin abincin ana hada shi da shayi mai zafi, wanda babu madara.
No comments:
Post a Comment