Wasu daga cikin mata ba su cika sha’awar kwalliya ba, musamman bakaken mata. Bakar fata ba ta cika fitar da ado a fuskar mace ba, saboda launi ko rashin sanin irin hoda da janbakin da ya dace da launin fatarta. A yau na kawo muku hanyoyi masu sauki da mai bakar mace za ta yi amfani da su wajen inganta kwalliyarta ta birge maigida. Kuma idan ta yi kwalliya, kwalliyar ta bayyana.
Fandesho: Ya kamata bakar mace ta san irin fandeshon da ya dace da launinta kafin ta s aya. Yana da kyau idan bakar mace za ta sa yi fandesho, ta sa yi launin da ya dan fi nata fatar haske kadan. Za a iya amfani da buroshi na fuska don shafa fandeshon. Amma hanyar da ta fi sauki, ita ce amfani da yatsu don shafa su.
Hoda: Yawancin ba kaken fata za ku ga suna fama da maikon fuska. Amma akwai abubuwan da zai sa su rage gumin fuska ko maikon fuska wadanda na yi bayani a baya. Yana da kyau idan bakar mace ta tashi sayen hoda, ta sayo mai kyau, kuma kada ta bi araha. Kuma yana da kyau ta shafa hoda mai launin fatarta ba wanda ke dauke da launin dorawa ba. Idan aka sayi hoda mai tsada takan maye gurbin fandesho don kyau. Ina bai wa mata shawarar sayen hoda mai tsada domin kara musu kyau.
Blush: Na san za a yi mamaki idan an ce bakar mace za ta iya sanya blush. Lallai za ta iya domin blush na kara mata kyau. Ina son a san cewa ba kowane launi ba ne ke yi wa bakar mace kyau a blush ba, illa jan launi ko mai kama da shi.
Jambaki: Yin amfani da launuka daban-dab an na inganta kwalliyar mace, amma shin an san wane irin launi ya dace da bakar mace? Idan bakar mace ta yi amfani da jambakin da bai dace da launinta ba, ana ganin ta za a ga kamar ba ta da lafiya, ko ciwon sanyi ya kama ta. Za a iya amfani da jambaki, mai kama da ruwan kasa. Bayan haka, sai a dora wa lebban lip gloss don sanya lebba sheki.
Gazal da adon ido: Tunda fatar baka ce, za a iya sanya “eye shadow” mai yawa a kan ido. Za a iya shafa launin zinari ko ruwan hoda ko launin azurfa (pink or silber). Bayan an gama, sai a sanya gazal mai sheki a ido domin bayyana adon mace.
No comments:
Post a Comment