Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

YADDA AKE SAUKAR DA VIDEO DAGA YOUTUBE 1


YADDA AKE SAUKAR DA VIDEO DAGA YOUTUBE 

Assalamu Alaikum barkan mu da warhaka barkan mu da sake saduwa a cikin sabon shirin mu yau insha Allah zamu nuna muku yanda zaku saukar da video daga youtube ta hanyar amfani da wayan salula cikin sauki.

Kafin mu zayyno muku bayanin hanyoyi da ake bi domin a saukar da bidiyo daga dandalin zumunta wato YouTube, ya na da kyau mu fahimci wadansu ka’idoji da dokokin saukar da abu daga shi wannan shafin na YouTube. Su dai wannan kamfani wanda aka fi sani da YouTube mallakar babban ma’aikatar nan na Google ne, a hanlin da muke ciki a yanzu babu wani daki ko shafi a duniyan nan da ya ajiye hotuna masu motsi wato video kamar YouTube, haka kuma shi ne babban shafi wanda aka fi ziyarta domin kallon hotuna masu mosti (video), kuma shi ne shafi na uku a ziyarta a duk shafukan da suke intanet. Domin an ƙiyasta sama da mutane biliyan daya (1 billion) suke amfani da wannan shafi na YouTube haka kuma a shekara ta 2014 kamfanin ya sami ribar kudi zunzurutun dalar Amurka biliyon 4 (4 Billion USD), haka kuma kamar yadda kamfanin dubawa da yin hasashe na DMR (Digital Marketing Statistics) su ka fadi cewar a kullum ana kallon bidiyo biliyan 4 a kowace rana. A wuraren Satumbar 2011, kamfanin yayi wani alkawari da har yau bai cika ba, na cewar za su saki wata manhaja wacce zata ba mutane masu amfani da wayar komai da ruwanka damar kallon bidiyo a YouTube ba tare da amfani da fasahar intanet ba, matuƙar ka bude shi bidiyon kafin ka kashe intanet din. Wannan yunƙuri na su, har yanzu dai bai tabbata ba. Amma kuma idan ka dubi mafi yawancin bidiyon da yake cikin kwamfutocin mutane da wayoyinsu za ka samu cewar ana samun su ne daga YouTube. To, haka abin yake, domin kusan kafin a fara samun makarantu masu zaman kansu a intanet, mutane da dama suna daura karatukansu a shafin YouTube domin jama’a su kalle su. Shi yasa YouTube ya zama wani dausayin alheri da kuma tsibiri na sharri. Domin kusan dukkanin wani ilimi da mutum yake son ya koya zai yi wahala a shiga cikin shafin YouTube bai same shi ba. Wani lokutan ma shi wannan shafin manyan gidajen jaridu da gidajen yada labarai na talabijin suna amfani da shi wurin daura shirye-shirye domin jama’a su yi amfani da shi ko kuma su sake kallonsa bayan an gama yinsa.
Shi yasa kowane irin bidiyo ake samun shi kai tsaye a dandalin YouTube, kama tun daga na karatu, wasanni, nishadi, fadakarwa da dai sauransu, kuma dukkaninsu ana samun masu tsawo da matsakaita. A wani lokaci zaka samu mutum daya ya daura bidiyo sama da dubu biyu a shafinsa, kuma ka samu yana da mabiya ko masu kallo sama da miliyoyin adadi.



TAKAITACCEN TARIHIN KAFA KANFANIN YOUTUBE

YouTube na daya daga cikin shafi a Intanet irin wadanda ake kiran su da video-sharing website a turance, wato shafukan da ake saka bidiyo domin wadansu su kalla a fadin duniya, ya na da Hedkwata a San Bruno da Jihar California ta kasar Amurka. Wadansu matasa su uku Steve Chen, Chad Hurley da kuma Jawed Karim su ne suka kiriro shafin a 14 ga watan Fabrairu 2005 bayan da suka bar aiki a wani kamfanin hada-hadar kudi a intanet mai suna PayPal. Tun daga shekarar 2005 zuwa 2006 su ne suke da alhakin mallakar komai a shafin YouTube har zuwa lokacin da kamfanin Google ya ga muhimmancin wannan shafi da yadda ya sami karbuwa a wurin mutane a fadin duniya, ya siye shi da kudi mai yawan gaske wuri na gugar wuri har dalar Amurka Bilyan 1 da Miliyan 650 ($1.65 billion) a watan Satumba 2006. Chad Hurley, Steve Chen, sai Jawed Karim Daga dama: Chad Hurley, Steve Chen, sai Jawed Karim Shafin wanda yake ba mutane damar su daura bidiyo domin mutane su kalla ko domin su yada shi a shafukan intanet ko kuma lika shi a shafukan zumunta na yau da kullum. Ana amfani da zarin abin kallo na kwamfuta da wayoyin domin iya kallon su, kamar tsarin WebM da H.264 da MPEG-4 da AVC da kuma Adobe Flash Player. Ana samu bidiyo daban-daban kamar na wasanni, shirye-shiryen gidajen yada labarai, bidiyon wakoki, fina-finai, karatuka, bidiyo domin ilmantar da dai sauransu wand aba zan iya lissafowa ba. Mafi yawancin bidiyon da suke YouTube gama garin mutane ne suka daura shi, amma kuma ana samun gidanjen yada labarai manya sanannu suna amfani da shi, kamar irin su CBS, BBC, VOA da GOTEL da dai makamantansu. Wanda bai yi rigista da kanfanin YouTube ba zai iya kallo ne kawai, amma wanda yayi rijista zai iya kallo, zai iya daura shima na shi bidiyon domin wadansu su kalla, zai iya kulla alaka da wani mai daki a YouTube duk lokacin da ya daura wani sabon bidiyo a sanar da shi kai tsaye (Subcribe), sannan zai iya yin tsokaci (comment) ga bidiyon da aka bayar da damar yin tsokaci a kai. Dukkan bidiyon da yake YouTube babu matsala wurin kallonsa matukar bai dauki hotuna na tsaraici ko na wanda yake dauke da hotuna masu hatsari, kamar kisa ko kuma abin da bai kamata masu karamin kwakwalwa su kalla ba. To irin wadannan bidiyo dole sai ka fadawa YouTube cewar kai ka wuce shekaru 18 kafin ka ga irin wadannan bidiyoyin. Shafin na YouTube yana samun kudaden shigar shi ta hanyar saka talla da yake yi a kan bidiyo da mutane su kallo, kuma sun ba masu bidiyon damar mallakar kashi 55% na kudin da ake biyansu. Misali a shekarar 2013 kamfanonin da suke ba YouTube talla su na biyan su dalar Amurka $6.60, idan aka kalli bidiyo ko kuma tallansu har sau 1000, wanda yake nuna cewar duk wanda ya amince da YouTube su saka talla a kan bidiyon da ya daura a shafinsu zai iya samun 0.5x $7.60×55%=N2.09 wannan tsarin an yi amfani da shi a shekarar 2013. Shafin na YouTube yana iya kokarin ya ga ya hana mutane daura bidiyon da baka da hakkin mallaka, wato irin na satan safage wanda kusan da yawa daga cikin bidiyoyin da suke YouTube wadanda suka daura shi ba su suke da hakkin mallakar shi ba.



SHIN DAIDAI NE MUTUM YA SAUKAR DA VIDEO A YOUTUBE?

Eh Babu laifi idan mutum ya saukar da bidiyo daga YouTube domin yayi amfani don karan-kansa ba tare da juyashi ba ko kuma ya canza shi zuwa wata hanyar ba. Amma laifi shi mutum ya saukar da kowane irin bidiyo a YouTube sannan ya yi amfani da shi a wani gidan talabijin ko kuma ya gurza shi ko kuma domin sayarwa. Kamar yadda kamfanin na google ya fadi a shafin shi na sharadin amfani da bidiyon YouTube sun rubuta kamar haka, “ Ba a yarda kayi amfani da Video nan ba sai domin amfanin kanka, ba na neman kudi bane, ba za a diba ba (copy), ba sake gurzashi, ba rabashi, ba nuna shi a gidajen talabijin, ba yin kasuwanci da shi, kada ayi amfani da wani bangare nashi sai da izini rubutacce zuwa ga YouTube ”. Daga jin irin wannan sharadi yake nuna mana cewar idan mutum zai saukar da bidiyo daga YouTube kuma yana son yayi amfani domin nishadantar da kansa ko kuma ilmantan da kansa, to babu laifi. Haka idan muka dubi zuwa ga amfani da shi ta wadansu kafafe, sai muga hatta yadda mutanen mu suke saukar da bidiyo daga wannan gida kuma suyi ta gurzashi, wannan kai tsaye laifi ne. Shi ya sanya daga cikin dokokin amfani da shi, sun fadi cewar idan mutum ba zai yi amfani da intanet ba ne, ya kalla kai tsaye, to shima ba su yarda ya saukar da shi ba domin kallo. Saukar da bidiyo daga YouTube yana kawo wa wannan kamfani cikas ga harkokin kasuwancin su. Mutane da dama su na yawan tambayar mu shin, irin waɗannan shafuka kamar google, ko facebook, ko YouTube mene ne ribarsu? Sai mu fada musu cewar shigar da muke yi suna amfani da shafukan su, shi ne ribar su, domin manyan kamfanoni na duniya suna yin la’akari da yawan mutanen da suke shiga dakuna a intanet, kuma wannan dalilin yake sanyawa a basu talla.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive