Na hakura da aikin banki sakamakon daukar dogon lokaci da aikin yake yi wa ‘ya mace, hakan ne ya tilasta min hakura da wannan fannin inji malama Hauwa Suleman.
Ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir, inda ta bukaci matasa mata su maida hankali wajen neman ilimin zamani domin a dama da su kamar yadda zamani ke sauyawa.
Hauwa ta kara da cewa ta so ta karancin aikin jarida amma kamar yadda al’adar makarantu ta ke a Najeriya, ya sa ta sami gurbin karatu a fannin ilimin zamantakewar al’umma wato Sociology.
Kammalawarta ke da wuyu ta sami gurbin aiki a banki, wanda daga bisanai ta samu canjin aiki zuwa aikin gwamnati, ko da yake ta ce bata fuskanci gwagwarmayar rayuwa ba ko a fannin aiki da makamanta haka.
Daga karshe ta ce a lokacin da take karatu bata fuskanci wata matsala ba illa ta zirga-zirga daga gida zuwa makaranta, sai kuma nbangaren aiki inda ta ce takan fita aiki a wancan lokacin daga karfe bakwai na safe sai bakwai na dare wani lokacin ma har a wuce bakwai lamarin da ya tilasta mata hakura da aikin.
No comments:
Post a Comment