Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

YADDA AKE SAUKAR DA VIDEO DAGA YOUTUBE 2


SHIN MENE NE YA SA BIDIYO YAKE DA CIN MB?

Dalili kuwa shi ne domin bidiyo hotuna ne aka tara su a wuri guda. Yadda abin ya ke shi ne, duk wani bidiyo da mutum ya gani tun daga dakika daya zuwa awanni daga hoto daya ne zuwa hotuna 25 zuwa hotuna 60. Idan ka duba na’urar daukan hoto misali Camera ta wayarka, zaka ga daga bayan an rubuta lamba a gaban lambar an rubata Pixel, misali 2 Mega Pixel. Wannan megapixel sinadari ne da ake auna kyau da girman da Kamara zata iya daukar hoto da shi. Idan aka ce kamarar wayar ka ta na da 5-megapixel to ana son ka sani cewar wayar ka zata iya daukan hoto guda wanda sai an sami digo miliyan biyar a jikinshi. Shi daman Pixel a ilimin daukan hoto na nufin digo duga ko kuma rami guda da kala zai iya zama na hoto a cikinsa. Saboda haka, idan aka ce wayar mutum ko kuma kamarar shi tana daukar hoto mara motsi guda daya wanda ya kai nauyin 2Mb, to idan zata dauki bidiyon dakika guda sai ka hada 2mb x 25 = 120mb. A takaice duk mafi yawan bidiyon da muke kallo suna da zubu iri biyu ne, PAL da NTSC, bidiyon da aka daukeshi da fasahar PAL a kwane dakika ana samun hotuna 25, wanda kuma aka yi amfani da fasahar NTSC ana samun hotuna 29 zuwa 30 a kowane dakika guda. Ba a maganar cewar lokacin da kamarar take daukan hotunan tana kuna hadawa tare da sauti wanda shima yana da nasa nauyi. Wannan shi ne dalilin da ya sanya bidiyo ya ke nauyi kasancewar tarin hotuna ne da sauti a hade a wuri guda kuma yake aiki.


MENE NE DALILIN DA YASA BA MABALLIN SAUKAR DA BIDIYO KAI TSAYE A SHAFIN YOUTUBE WATO DOWLOAD?

Kamar yadda muka fadi cewar a shekarar 2014 kamfanin google ya sami ribar dalar Amurka biliyan hudu wanda yake daidai da Naira Biliyan Dari Tara (900,000,000,000) ta su bidiyoyin da ake kallo a shafin YouTube. Wannan ribar ta samu ne saboda talla da yake bayyana a jikin bidiyo lokacin da mutum yake kallo. Wannan shi ne ma dalilin da ya sanya wani lokaci idan mutum yana son kallo a YouTube sai ya jira na ‘yan dakikoki biyu zuwa uku domin kallon talla kafin ya baka zaɓin ko ka ci gaba da kallo ko kuma ka wuce zuwa ga shi bidiyon da ka nemi ka kalle shi kai tsaye. Matsalar nan ita ce, idan mutane suka sauke shi bidiyon kun ga babu yadda za’ayi kamfanin su sami kudin su, dalilin haka ya sanya su kamfanin basa so mutum ya ce zai saukar da shi. Ko ba mu yi dogon bayani ba, kasan cewar da dukkanin bidiyoyin da suke cikin wayoyinmu za a barsu a shafukan da suke sai dai kawai mukalla a sama da kudaden da za su samu sai ya ninka wanda suka samu a shekarar 2014. Amma dai duk da haka mutane da yawa suna ta ƙoƙarin su ga yadda za ayi su saukar da wadannan bidiyoyi a kwamfutocinsu da wayoyin domin su iya amfana da su a wani lokaci.

            Youtube asalin sa a bude ne dan kalllo ba dan saukarwa zuwa cikin wayan salula ba amma wasu lokutan akwai wasu kwararan dalilai da mutane da dama suke son saukar da video daga youtube saboda kalllo lokacin da basu komai, koma me dalilin akwai hanyoyi da dama yanda zaka saukar da hoto mai motsi wato video daga youtube a wayan salula ko kuma kwanfuta.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive