Masu iya Magana kan ce babu nakasasshe sai kasasshe, Fiddausi Lawal, wata mai bukata ta mussamam ta ce ta fara fuskantar matsalolin rayuwa tun tana makarantar firamare.
A sanadiyyar matsalar da take tattare da ita, Fiddausi bata samun damar lokacin hutun cin abinci da ake badawa a makaranta a okaci guda tare da na ragowar 'yan makaranta.
Hakan bai karya mata gwiwa wjan ci gaba da karatu ba, ta kara da cewa bayyan kammala karatun sakandire, ta jajirce akan ra'ayinta na ci gaba da karatu duk kuwa da cewa ta fuskanci matsaloli da dama inda wasu daga cikin malamanta ma, basa saurara mata baya ga dawainiyar da wasu daga cikin dalibai ke yi na jigila da ita.
Malama Fiddausi, ta kara da cewa a mafi yawan lokuta mutane hudu ne dawainiyar daukanta domin hawa da sauka daga bene a makaranta. A cewarta, yayin da take makaranta ba ta da wata hanya ta mussamam domin samun taimako irin na masu bukata ta mussamam.
Fiddausi ta ce duk da bukata ta mussamam da Allah ya nufe ta da ita, hakan bai hana mata karasa karatunta ba domin kuwa a yanzu tana da digirinta na biyu kuma a yanzu ma ta samu gurbin aiki a ofishin babban akanta na kasa baiki daya.
No comments:
Post a Comment