Hanyoyin da za a bi don rage kibar jiki...
Assalamu alaikum matan gidan nan. A yau na kawo muku wata hanyar da za a bi domin inganta kwalliya. Babbar magana a nan ita ce rage kibar jikinmu, domin kiba ba karamar kara wa mace muni take yi ba. Ko da akwai hanci kibar sai ta shanye hancin. Idan har ana son a yi kyau, idan an yi kwalliya, sai an taimaki kai wajen rage wannan kibar. Ba a rana daya aka hada wannan kibar ba. Don haka sai an yi hakuri da juriya kafin a rage kiba. Ga kadan daga cikin hanyoyin da za a bi domin rage kiba don taimaka wa kwalliyarmu.
· A dage wajen cin kayan lambu; kamrsu ganye da kabeji da sauransu, domin suna taimakawa wajen rage kibar jiki.
· Ka da a bar ‘y a’yan itatauwa a baya; yawan shan ‘ya’yan itatuwa kamar su lemu da mangoro da ayaba da kankana da sauransu na taimakawa wajen rage kiba, har ma su inganta fata da kwalliya.
· A rika shan ruwan lemun tsami da zuma a ruwan dumi idan gari ya waye kafin a ci komai.
· Ka da a zauna da hada maiko, alhalin ba a motsa jiki, sannan sai a ce ana son rage kiba. Don haka sai a dage da motsa jiki ko da kuwa ‘yar gala-gala ce ake yi za ta taimaka.
· Akwai wata ‘’yar na’ura ko damarar ‘tummy trimmer’ da mata ke amfani da ita domin rage kibar tumbi; idan an sanya wannan abu za a rage yawan ci, sannan a rage kibar tumbi.
· Bayan an yi wadannan abubuwan da na lissafo, tabbas idan an yi kwalliya za a y i kyawun gani, a fito fes sosai. Kuma za a ga kowace irin kwalliya aka yi sai a ga an yi kyau tamkar an rage shekaru. An ce dai ‘in ana da kyau sai a hada da wanka.
No comments:
Post a Comment