Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

ABUBUWA SHIDA DA BA SU KAMATA A SHAFA A FUSKA BA




Abubuwa shida da ba su kamata a shafa a fuska ba...

mayukan wanke gashin ka Abubuwa shida da ba su kamata a shafa a fuska ba... Fuska na daya daga cikin wuraren da yakamata a kula da ita domin da zarar an hangi mutum itace abin da za a fara kalla. Mata da dama domin neman gyara sai su shafa abubuwa da dama domin gyaran fuskarsu ba tare da sanin ko wannan abin ya dace da fuskar ko kuma bai dace da ita ba. Akwai abubuwan da idan an shafa a fuska maimakon su kawo wa mutum waraka sai su kara feso kuraje a fuskar. Don haka zan lissafo su domin a kula.

·        Bai kamata idan an zo fesa turaren gashi ya taba fuska ba. Domin idan wannan turaren ya taba fuska yakan janyo gautsin fata da kuma nuna tsufa ga fuska. Sai a kula.
·        Kada a shafa man ‘lotion’ ko wane iri a fuska. Yawan shafa man na toshe ramukan gashi dake fuska kuma hakan yakan haifar da fesowar kuraje.
·        A daina shafa turaren hammata a fuska (deodorant). Kamar yadda ba za a iya daukar tawul din fuska a goge hammata, haka kuma bai dace a shafa turaren hammata a fuska ba koda wannan ya kasance mai yawan gumi.
·        Man wanke gashi ‘shampoo’ na dauke da sinadaran da ke iya bata fuska. Don haka, sai a kula idan an zo wanke gashin ka, kada a hada kumfar wajen wanke fuska domin hakan yakan sanya fuska dada tsufa da kuma bushewa.
·        Idan an zo yin hadin man wanke gashi kamar man ‘mayonnaise’ sai a kula kada ya taba fuska. Idan ya taba fuska, yana hana fuska sakewa har ya haifar da fesowar kuraje.
·        A kula wajen amfani da man da ake shafa wa gashi ‘hair dye’ a fuska a matsayin ‘eye shadow. Yin hakan na haifar da fesowar kananan kuraje da za su iya bata fuska.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive