Amfanin kankara a fuska da kuma fatar jiki...
Nasan za a yi matukar mamaki yadda kankara ke da amfani a fuskarmu da kuma fatar jikinmu. Ina so a san cewa, amfani da irin wannan sai dai lokacin zafi. Domin a wadannan lokutan ne ake yawan gumi da kuma jin zafi. Kamar yadda idan an shiga rana ana bukatar abu mai sanyi domin samun sauki a jiki. Haka kuma fatar fuskarmu da kuma fatar jiki. Yin hakan na hana fesowar kurajen zafi a jiki da kuma fuska.
· Idan an shiga rana ko kuma an dawo daga aiki a lokacin zafi, a samu kankara a shafa a kan ido. Yin hakan na sanya idon farfadowa daga wahalar da ya sha sakamakon zafin rana.
· Ga wani sirri; kafin a fara kwalliya, yana da kyau a samu kankara a dan goga a fatar fuska kafin a shafa komai a fuska. Yin hakan na sanya kwalliya dadewa a fuska.
· Zafi ko kunar rana na sanya mutsikewar fuska ba tare da sanin yin hakan ba. Yana da kyau idan an dawo gida a shafa kankarar a fuskar domin hana kunar rana fita a fuska. Kuma za a ji saukin al’amarin.
· Yana da kyau wanda ke da maikon fuska yana amfani da kankara, domin yin hakan na rage girman ramukan gumi da ke kan fatarmu. Hakan kuma ke kawo raguwar fitar maikon jikin, wanda ke haifar da kuraje a fatar jiki ko fuska. A saka kankarar a zani mai kyau a nade shi a rika shafawa a fatar jiki da fuska har sai ta narke.
· Domin samun fata mai ha ske da sheki, za a iya wurga kankarar a cikin ruwan ‘ya’yan itatuwa kafin a shafa a fuska. Yin hakan na taimakawa wajen inganta shekin fata da kuma haskakata.
No comments:
Post a Comment