A shirinmu na mata a yau dandali ya waiwayi dabi'ar nan ta samari da rashin kyauta ga 'yan matansu a wannan karnin.
Acewar da dama daga cikin wadanan 'yan mata, samarin yanzu hannun jarirai gare su, ta inda basa kyautar nan da aka saba tsakanin samari da 'yan mata.
Kamar yadda suke cewa, sai dai ma su yi dabarar marairaicewa, tare da kawo wani uzuri da zasu karbe dan canjin da ke hannun 'yan mata. Inda suke cewa, mafi akasari a yanzu suna sana'o'in dogaro da kai ne, domin hucewa kansu bakin cikin rashin, kamar yadda Hauwa Adam ke cewa.
Ita kuwa Amina cewa ta yi, lokacin da samari ke da kyauta ya jima da wuce a yanzu, yanzu dai akwai 'yan tayin hira ne, ba samari ake da su ba.
A nasu bangeren wani matashin saurayi, Suleiman Babangida, cewa yayi tun farko bai dorawa kansa abinda ba zai iya ba, domin akwai lokacin da ya je zance aka yi rashin sa'a, kudinsa sun kare budurwarsa ce ta agaje shi, da kudin motar komawa saboda yadda suka fuskanci juna a cewarsa.
To wai rashin sanin darajar 'yan matan ne yasa samari basu basu wani abun kyautatawa ko kuwa rashin abub hannu ne? Ka za'a iya cewa 'yan matan suna nema abubuwa da yawa ne a wajen samarin nasu?
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
No comments:
Post a Comment