Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Beans Buns

Duniyan FAsaha
Beans Buns
Ingredients

Wake
Kwai
Garin bread
Nikakken nama
Magi,gishiri
Curry
Albasa
Mai
Tafarnuwa

YADDA AKE
Ki samu waken ki me kyau mara kwari ki
gyarashi,sai ki surfashi ki wanke ki fidda
hanncinsa tas,sai ki dora ruwa a tukunya kisa
waken ki dafa shi, sai yayi laushi,amma ba
tubus ba,sai ki sauke,
dama kin tafasa namanki da albasa da magi
da tafarnuwa,kin dakashi,sai ki soyashi sama
sama,karki bari ya kandare,
sai ki dauko wannan waken ki tukeshi kamar
tuwo,kisa magi da gishiri a ciki idan kina
bukatar curry sai kisa a ciki ki cakuda,
sai ki dinga diba kina sa naman a tsakiya kina
curashi kamar ball kina barbadeshi da garin
bread kina ajewa har ki gama,
san nan ki fasa kwai kisa magi ki kada ki dinga
dauka kina soyawa a mai me zafi,
ki gwada yana da dadin ci kuma ga kamshi
daga nesa.

Wow baa bawa mai rowa
Matan gida muna jiran ganin pics

Duniyan Fasaha

ISLAH TASIU YAU
MRS JAMEEL
+2349063541142


mawallafi:

sunana *ISLAH TASIU YAU* wacce ake qira da *Mrs jameel ko Ummu amjad* Ni haifaffiyar kano ce an haifeni a shekara ta 1996 nayi makarantar primary da secondary a spring int school Yanzu ina zaune garin daura da aure Ni marubuciya ce Kuma ina karatun littafai nima ina karatu yanzu a health technology daura inda nake karantar *chew* Ina daya daga cikin members na *DUNIYAN FASAHA* Kuma ina cikintane Dan bada gudunmawa ga ilahirin al'ummar musulmai Daga karshe ina fatan abunda muka sa gaba Allah ya bamu ikon cikawa Ya bamu ikon isarwa lafiya,ya yafemana kura-kuren da mukayi baki daya

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive