Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

YADDA AKE YIN BINCIKE WATO SEARCH DA GOOGLE SEARCH


Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na Duniyan Fsaha. Insha Allah yau zamuyi bayanine a kan duba abu a google, Ba kawai zaka buɗe shafin google bane ka rubuta suna ko kuma wani abu da kake nema ba, shine kawai hanyar da zaka bi ka yi bincike. Google shine gidan da ya fi ko’ina shahara a internet kasancewar shi daya daga cikin gidajen da suke daukar dawainiyar fito da amsoshin abubuwan da mutane suke nema daga shafukan mutane. Google kamfanine da ya shahara a bakin duk wanda yake amfani da internet, mu samman wanda suke yawan bincike da neman bayanai, amma kuma google ba bincike kawai ake yi a cikin su ba, su na da ayyuka da dama da yake yi, wanda suka hada da kalanda, da akwatin ajiyar imel, dakin ajiyar takardu, youtube, video, biyan kudi wa masu aiki da blog, document, canza harshe, blogger, photos, shopping da dai makamantansu. Abu na farko bincike mai sauki, wanda ku san kowa shi yafi amfani da shi, sai dai kuma ana amfani da shi cikin kuskure, shine zamu yi dan gyara a kai. Kashi na biyu kuwa zamu zurfafa binciken ne, ta wajen amfani da zurfafan hanyoyin yin bincike a shi google search engine, ta yadda yin amfani da wannan hanyar zai saukaka matuka da kuma fitar da sakamako mai inganci. Kashi na uku wanda kuma shine na karshe shi kuma zamu yi bayanin hanyoyin da ake bi a binciken hotuna, video da kuma wurare a duniya baki daya. kamar yadda mafi yawa daga cikin mu suka sani, duk wanda yake da waya ko kuma yake da computer da yake son yayi bincike shine ya shiga google. wanda kuma bai san yadda zai yi ba to, zai rubuta www.google.com a wurin da ake rubuta adireshin shafukan internet wanda aka fi sani da Address Bar a cikin browser, da zarar ya rubuta zai bude mishi shafin farko. A dai dai lokacin da mutum ya rubuta abinda yake nema a google, misali ya rubuta Duniyan Fasaha to bayan ya rubuta tambayar shi sannan ya latsa search to ya sani google zai shiga cikin taskar da yake ajiye bayanai na dukkanin shafukan da suke cikin internet a fito da kalmar Fasaha da kuma kalmar Duniyan sannan kuma zai yi kokarin ya fito da in da ya same su a hade. Shi yasa idan mutum ya shiga internet domin yayi bincike kuma ya shiga dakunan bincike irin su google da zarar ya rubuta tambaya sai kawai yaga sakamako a kalla miliyan hamsin, wanda kai da kan ka mai karatu ka sani cewar ba yadda za ayi tambaya daya ace tana da amsa sama da miliyan daya koma ace dukkansu daidai suke. Shi yasa yana da kyau masu karatu su sani cewar ba dukkanin sakamakon da ka yi binciken ta a google ba ne yake zama cikakken amsa ba. Dukkanin wasu kalmomi da ka rubuta cikin dan ramin da google suka bayar a rubuta zai fito maka da amsoshin iya adadin kalman. Misali da mutum zai rubuta how can I write English” to abinda google zai maka shine duk inda aka rubuta kalmar how” a internet zai fito da ita. Haka kalmar can zai fito da dukkanin shafukan da aka rubuta wannan kalmar, haka zai ta fito da ko wane kalma daya bayan daya, sai ka samu amsa sama da miliyan goma amma kuma da wuya ka sani amsa tare da wannan cikakkiyar jumla kamar yadda ka rubuta ta. Da wannan dalili ne yasa su kansu kamfanin google suka fito da wasu hanyoyi da zasu saukakawa masu bincike a yanar gizo wajen samun gamsasshiyar amsa. Sabo da haka, zamu dauki wadannan hanyoyi daya bayan daya muyi bayanai akan su domin mu saukaka muku kuma wajen yin bincike a google.

BINCIKEN JUMLA WATO SENTENCE

Binciken kalma a google kamar yadda nayi bayani a baya kan iya fitowa da sakamako mai yawa wanda kuma basu da dangantaka da abinda ake nema. Amma kuma idan ya zo ta bangaren kasan me kake nema, to, akwai abubuwan da zaka kiyaye wajen binciken. Duk wanda ya san me ya ke nema kamar kana son ka nemi wata jumla a yanar gizo ko kuma wani shugaba yayi wani jawabi kuma ka haddace yadda ya fadi kalmar kuma kana son ka karanta sauran labarin to, google sun bayar da hanyoyin da zaka bi idan ka hada da kalmar da kake bincike zai bada amsarka daidai. Quotation Marks (Baka biyu) “ ” duk wanda zai yi bincike wani abu da yake son gani to sai ya saka shi a cikin baka biyu. Misali “Duniyan Fasaha” ko “Hankali ke gani ba ido ba” saka wadannan tambayoyi a cikin baka biyu zai dawo maka da amsar ka a duk shafukan internet ba tare da ya kakkatse zuwa kalmomin ba. Phrase Connector: sune hyphen ( – ) ko slashes ( / ) ko period ( . ) ko equal signs ( = ) da kuma apostrophes ( ! ) wadannan alamomi su ake kira da phrase connector suma kamar yadda aka yi amfani da baka domin samun ainihin amsa, suma haka ake amfani dasu misalin duniyan-Fasaha ko duniyan.Fasaha ko hankali=ke=gani=ba=ido=ba da sharadin ka da ka bada sarari a tsakanin kowa ne kalma.

AMFANI DA LOKACI

Idan mutum zai binciki wani abu a internet kuma wannan abun ya kunshi lokaci, to, zaka iya yin amfani da abinda ake kira Date Range shi kuwa Date Range ana saka shine a wajen binciken abubuwan da aka san lokacin faruwarsu da kuma ana kokwanton daga lokaci kaza zuwa lokaci kaza ne abu kaza ya faru. Ko da yake shi amfani da wannan hanyar binciken tana da sharudda wanda sai an kiyaye su kafin a samu amsar da ake nema. Misali wanda yake son yayi binciken abinda ya shafi wani littafi wanda bashi da hakikanin lokacin da aka wallafa wannan littafi amma kuma yasan bai wuce daga shekarar 2014 ba zuwa 2016. To, da farko dole ya rubuta sunan littafin sannan ya rubuta shekarar da yake tunanin itace aka wallafa shi, sannan ya rubuta karshen shekara. Waye Sanadi daterange:2014-01-13..2016-01-13

AMFANI DA KALMOMIN CIKI (METADATA)

Wannan shi kuma tsari ne da kamfanin google suke baiwa masu binciken asalin kalma da ta ta’allaka ga shafu da suke da kalmomin ciki wato metadata, su metadata a takaice wadansu kalmomin da aka saka su a cikin shafukan internet domin saukakawa shi search engine saukin gano shafuka da abubuwan da shafukan suka kunsa. Misali duk lokacin da masu ilimin sanin yadda ake shirya shafukan yanar gizo “web designer” su ka kirkiri shafi to zai rubuta wadansu kalmomi da suke da alaka da wannan labarin da ke cikin wannan shafin. Kamar mutum ya rubuta labari game da computer kuma yayi magana akan abinda ya shafi Microsof Office, to, a wurin da ake rubuta shi metadata sai ya rubuta Kalmar Micrsoft, Windows, Office, Computer da dai wadansu ‘yan kalmomin da yasan mai bincike a internet zai iya rubutawa don neman sani. Wannan shine dailin da ya sa idan mai bincike ya shiga google domin yin bincike idan ya rubuta wata kalma sai yaga wani shafi ya bube amma kuma idan ya duba sama da kasan shafin zai ga babu wannan kalmar a ciki. To ita wannan Kalmar tana boyene a cikin kalmomin ciki “metadata”. To, wanda yake son ya binciki wani shafi amma kuma yana son shi shafin da ya ke binciken ya kasance a cikin sa ya kunshi kalmar kaza to zai iya yin amfani da tsarin metadata wajen yin binciken. Sannan wani Karin haske ma zai kuma iya kididdige lokacin da aka saka wannan bayani desertherald inmeta:modified:2006-01-01..2006-12-31 shima kamar yadda muke gani mun yi amfani da kalmar da muke nema, sai muka saka inmata wanda shi ya ke wakiltar google search engine, sannan kuma sai ka saka Kalmar modified wato lokacin da aka gyara ita waccan kalmar da kake nema, sannan ka saka kwanan wata. Wurin yin amfani da kwanan wata a wurin yin bincike a google mu kiyaye da yadda ake tsara date din, kwanan watan da zaka rubuta na farko dole ya fara da shekara sannan wata sannan rana kamar haka 2006-01-01.

AMFANI DA LAMBOBI:

Mutum na iya binciken abu a google ta hanyar amfani da lambobi wajen bincikensa. A misali mutum yana neman wani abu wanda kudinshi bai wuce kaza ba to zai iya amfani da wannan tsari wajen yin binciken. Phone $40..$90 idan ka rubuta haka to google zai fito maka da wayoyin hannu wanda kudinsu bai gaza dala arba’in ba kuma basu wuce dala casa’in ba.

TACE KALMOMI WAJEN BINCIKE

Wannan bangare kuwa shi zamu nuna mai karatun wasu ‘yan hanyoyine da zai bi wajen neman kalma da kuma wata kalmar da ke da dangantaka da kalmar farko, ko kuma ya son yayi binciken kalma amma kuma baya son kalma kaza ta biyo baya, ko kuma ya na son yayi binciken kalma amma kuma ta zo da kalma kaza tare da ita, ko kuma ya binciki kalma kaza amma kuma idan ba a samu wancan kalmar ba to wata kalmar ta zo.
KALMA1 OR KALMA2 (KALMAR FARKO KO KALMA TA BIYU)

Idan mutun na son yayi binciken kalma sannan kuma idan wannan kalmar bata samu ba to a nemo wata kamla sai ka rubuta a cikin ramin google search engine duniya or lahira rubuta kalmar or a tsakanin kalmomin guda biyu shi ke fadawa google cewar a nemo mini kalma kaza ko kuma kalma kaza.


KALMA1 -KALMA2 (KALMAR FARKO BANDA KALMA TA BIYU)

Idan mutum yana son yayi binciken kalma amma kuma baya son ya zama binciken ya hada da kalma kaza to zai rubuta a cikin ramin google search engine misalin Wannan bangare kuwa shi zamu nuna mai karatun wasu ‘yan hanyoyine da zai bi wajen duniya -lahira. Yin hakan ka fadawa google cewar ayi maka binciken shafukan da aka samu Kalmar duniya amma kuma kada a samu kalmar lahira a cikin shafin. Amma wurin rubuta wannan hanya mutum sai ya kiyaye kada ya raba lamar ragewa ( – ) da kalma ta biyu.

KALAM1+KALMA2 (KALMAR FARKO TARE DA KALMA TA BIYU)

Idan kuwa mutum na son yayi binciken kalmomi guda biyu lokaci guda, misalin yana son kalmar duniya amma kuma ya kasance an sami kalmar lahira a tare ko kuma a cikin shafi guda to sai ya rubuta kamar haka duniya +lahira wanda ya rubuta haka zai sami sakamakon shafin da aka samu kalmar duniya sannan kuma aka samu kalmar lahira a cikin shafin gaba daya. Shima kamar yadda na sama yake kada ka raba alamar hadawa ( + ) tare da kalmomin da kake bincike.

~KALMA (‘YAN UWAN KALMA)

Idan mutum na son yayi binciken kalma amma kuma yana son a nemo mishi kalmomin da suke da alaka da wannan kalmar to a nan zai saka alamar ( ~ ) a jikin ita kalmar. Misalin idan kana son wadansu kalmomi ne suke da alaka wajen ma’ana tare da kalmar education to sai ka rubuta kamar hama ~education yin hakan zai fito da dukkanin kalmomin da suke da alaka kalamar education wanda a turance ake kira da synonyms.

KALMA -KALMA (‘YAN UWAN KALMA TA FARKO AMMA BANDA KALMA TA BIYU)


Shi kuwa wannan binciken yayi kama da na samanshi, sai dai kuma banbanci tsakaninsu shine wannan kana bukatar a kawo maka kalmomin da suke da alaka da wannan Kalmar amma kuma baka son wanda suke da alaka da kalma ta biyu. Misalin ~examination - assignment wadannan kalmomi ne guda biyu masu alaka da junansu ta wajen ma’ana, to amma kuma idan ka saka irin wannan tambayar za a baka amsa da dukkanin kalmomin da examination yake da shi tare da alakanta kansa da shi, da kuma kin fito da kalmomin da suke da alaka da assignment. Wadannan sune a takaice abun da za mu iya baku wadanda suke shafi yin bincike tare da google search engine, Da fatar za a kasance tare da mu a darasi na gaba. Ga neman karin bayana ko tambaya zai iya aiko da ita kai tsaye zuwa ga: [email protected] ko kuma ta hanyan turo da tsako 09039016969.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive