Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

MUHIMMAN SHAWARWARI BAKWAI (7) GA MASU AMFANI DA BLOG



Assalamu Alaikum, tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. insha Allah yau zan bada wasu shawarwari wa masu rubutun ra'ayin kansu ta hanyan ranar gizo wato blog. zama daya daga cikin gwanayen rubutun ra'ayin ka ta hanyan yanar gizo wato blog ba karamin aiki bane, abu na farko mai dadi shine kasancewar kaine shugaba, wanda ke nufin ba zama daga safe zuwa dare ba, zakayi duk abun san ranka zaka kuma sa abun san ranka, son zama daya daga cikin jerin sunan masana kuma gwanaye wajen yanar gizo wanda ke dauke da wasu matsaloli da dama, musamman in kana tafiyar da komai da kanka na tsawon lokaci, yana da kyau ka fita dan ganawa da mutane, zaka iya hakan ne ta hanyan:-

1- Aiki a cafe
2- Halartan taron kara wa juna sani
3- Halartan taron sadarwa na kwanfuta koh na zamani

Ayan anan shine kada ka bari yancin rubutun ra'ayinka a yanar gizo ya zama maki yinka, insha Allah yau zan zayyano hanyoyin da na bi dan gujewa hawan jinin rubutun yanar gizo, yana da matukar amfani musamman a wannan zamanin namu na fasaha.

ABU NA FARKO

Daukan hutu a ayyukan yau da kullum
Daukan hutu a tsakin aiyuka yana da matukar amfani dan taimakawa ido daga hasken wutan kwanfuta koh na wayan salula, yana taimakawa wajen kore gajiyan kwakwalwa yana kuma taimawa wajen samar da karfin gwiwa dan karasa aiki daya rage misali daukan hutun minti hudu na tsawon aikin minti talatin. kada kayi kokarin cigaba da aiki sosai yana haifar da wasu matsaloli.

ABU NA BIYU

Yin aiki a wada taccen wutan lantarki

mafi yawancin masu rubutun ra'ayin kan su wato blog suna watsi da yanayin hasken wutan lantarki, wadun su sukanyi aiki a wurin da babu haske wanda hakan ba karamin illa yake kawo wa lafiyan idanunmu ba, hasken wutan kwanfuta koh wayan salula ba karamin illa yake kawo wa lafiyarmu ba, kayi kokarin daidai ta hasken wutan kwanfutanka dana dakinka sannan kayi kokarin bude tagogi dake cikin dakin.

ABU NA UKU

Kibta idanu

kayi kokarin yawai ta kibta idanu domin yawai ta aiki na tsawon awa goma 10 koh sama da haka yana kawo rashin ruwa a cikin idanu, yawan kibta su yana mayar dasu mazauninsu na da. masana sunyi ittikafin cewar yawai ta kibta idanu yana taimakawa ido sosai wajen aiki.

ABU NA HUDU

Zaban kayataccen wajen aiki

in kana aiki a offishi shine waje mafi inganci dan aiki saboda bazaka fuskanci wani matsala ba saboda an kayyadesa ne dan aiki. amma in kana aiki a gida yana da kyau ka kayyace wajen aiki, ka nisanci kanka daga yara kana’na da wasu ayyukan gida wanda zai na dauke ma tunani.

ABU NA BIYAR

Cire abun daukan hankali
kada ka hada ayyukan gida da na ayyukan yanar gizon ka sannan kayi kokarin cire duk wani abu da zai katse ka ko ya dauke maka tunaninka a yayin da kake aiki.

ABU NA SHIDA

Ka samar da allon rubutu
ka samar da allon rubutu a dakin ka dan zayyo shirin abubuwa da zakayi gaba, ka rubuta duk abubuwan da kake so kayi a cikin satin nan koma watan gaba daya, ka dage wajen lissafo abubuwan da zakacinma a cikin mako.
ABU NA BAKWAI WANDA SHINE NA KARSHE
KA NESANTA DA WAYAR SALULANKA

wannan yana daya daga cikin abu mafi muhimmanci a lokacin da kake yanayin rubutu, karan kiran waya koh alamar shigowar sako zai iya yanke ma tunani ko hankali abu mafi muhimmanci da nakeyi yayinda nake amfani dashi koh kuma amfani da kwanfuta shine katse layuka na, duk da cewar yana da amfani ya kasance a kunne amma kasancewar koda yaushe muna nan a kan chatting zai iya daukan hankali.


Wayannan sune wasu daga cikin shawarwari ga masu rubutun ra'yin kansu ta hanyar yanar gizo wato blog. Yanzu lokacinka ne, in kana so kayi kari a kan shawarwarin dana bayar zaka iya rubutawa a akwatin nuna ra'ayi wato comment box.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Za'a iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive