Matakan da za ki bi wajen yin zanen lalle
Sau da dama wadansu matan sukan shiga damuwa musamman ma idan suka zo maganar
yin zanen lalle, kasancewar sai su sha wahalar yin zanen lallen ba tare da ya yi kyau ba.
Idan ta wannan ne sai mu ce ki sha kuruminki, domin mun taho miki da matakan da za ki bi
wajen yin zanen lalle.
Tabbas yayin da kika zo yin zanen lalle akwai matakan da ya kamata ki bi, wanda idan har
kika bi matakan zanen lallenki zai zama abin sha’awa ga sauran mata.
Akwai hanyoyin da dama na yadda ake yin zanen lalle, amma akwai na zamani, wanda
kuma yake da sauki, ana yin wannan zanen lallen na zamani da wani sirinjin ko kwaroro da
ake kira ‘cone’. A Turance ana kiran salon zanen lallen da suna ‘Tube Henna’.
Kayan hadi:
Garin lalle
Lemon tsami ko kuma jus din ‘Lemon Juice’
Suga
Man Essential Oil
Cokalin karfe
Faffadar roba
Leda fara ko baka
Sirinjin ko kwaroron da ake kira ‘cone’
Yadda ake hada lalle:
- Ki samu lalle mai kyau da inganci, sai ki daka shi har ya yi laushi sosai. Daga nan sai ki
zuba shi a cikin faffadar roba.
- Daga nan sai ki samu lemon tsami kamar biyu, sai ki matse ruwan ki zuba shi cikin
dakkaken lallen, ko kuma ki zuba ruwan ju din ‘Lemon Juice’. Sannan ki gauraya ta hanyar
amfani da cokalin karfe.
- Bayan nan sai ki samu man essential oil, sannan ki zuba a cikin lallen da kika hada da
lemon tsami ko kuma ruwan jus din ‘Lemon Juice’. Daga nan sai ki gauraya sosai. Ki
tabbatar da ba a samu kulli-kulli a ciki ba. Amfanin lemon tsami ko jus din ‘Lemon Juice’,
shi ne, sukan fito da launi sosai yayin da aka shafa lalle. Man essential oil na sanya lalle ya
ratsa fata, ya kuma sanya zanen lalle ya fito sosai.
- Daga nan sai zuba suga walau hakan ta, ko kuma ki jika ta da ruwa kadan. Amfanin
suga shi ne, takan sanya lalle ya yi danko, a lokaci guda ta hana lallen kakkaryewa,
sannan takan sanya lallen ya kama wajen da aka shafa lallen.
- Daga nan sai ki samo faffadar ledar da za ki rufe robar da kika kwaba lallen. Kada ki
bari iska ta shiga, domin idan kika bari iska ta shiga zai kawo nakasu wajen fitar launin
zanen lalle.
- Idan har kina so zanen lalle ya fita sosai da kuma kyau, to ya kamata kafin ki shafa lalle
bayan ki kwaba shi to ki bar shi ya yi awa 24.
- Bayan nan sai ki zuba kwababben lallen a cikin sirinjin ko kwaroron cone, sannan ki yi
zanen da kike so, walau fulawowi ko zanen wani abu daban.
mawallafi: Muhammad Abba Gana
Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.
No comments:
Post a Comment