Yadda za ki yi amfani da fiya wajen gyaran fuska
Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na Duniyan Fsaha. Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya, Sau da dama mutane sun dauka amfanin fiya shi ne a ci kawai, ba tare da sun fahimci ana amfani da ita wajen gyaran jiki da fuska ba. Dalilin da ya sanya a wannan makon mukataho miki da matakan da za ki bi wajen amfani da fiya don gyaran jiki da fuskarki ke nan. Amfani fiya ga jiki:
- Ana amfani da fiya ga busasshiyar fata don kawo danshin fata. Tana dauke da sinadaraimasu yawa wadanda suka hada da bitamin K da C da Copper da Iron da sauransu.
- Fiya tana dauke da sanadarin da bitamin A da kuma Glutamine wadanda suketaimakawa wajen kawar da matattun kwayoyin halittar cikin fata.
- Laushin fata: Fata takan tsotse man da yake cikin fiya, wanda hakan yakan sanyawaman ya ratsa kofofin fata, inda fata kuma takan tatse sinadaran da suke dauke a cikin fiya,wannan sai ya sanya fata ta yi laushi da kuma dadin gani.
- Mayar da tsohuwa yarinya: Fiya tana dauke da sinadaran da suke kone kwayoyincututtukan da suke kodar da fata, wanda hakan sai ya sanya fata ta rika sheki da kumalaushi, har a rika taken ta mayar da ke yarinya.
- Hasken rana yana dauke da sinadaran da suke kodar da fata ko kuma su sanya saurintsufa, amma sakamakon sinadarin da fiya take dauke da shi, sai ya zamanto ta kare fatada sinadarin hasken rana.
mawallafi: Muhammad Abba Gana
Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.
No comments:
Post a Comment