Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

MADARAR WAKEN SUYAMADARAR WAKEN SUYA

_Abinda zaki Nema_

1.Waken suya
2. Sugar
3. Flavor
Yanda ake yi
1 .Da farko zaki gyara waken ki ki cire tsakuwa
da dauda, sai ki jika shi ya
kwana.

2. Da safe sai ki wanke ki rege, sai ki markada
ko ki kai a markado miki

3. Idan kin gama sai ki tace ruwan ki cire
dusar. Ki yi amfani da matacin koko
ba Rariya ba

4. Sai ki dora tacaccen ruwan a kan wuta ki
barshi yayi ta dahuwa har sai gafin
sa ya fita

5. Ki sauke ki barshi ya sha iska, sai ki zuba
flavor irin kanshin da
kike so da kuma sugar dai dai misali

6. Ki saka a fridge yayi sanyi
Ga sauki, ga dadi, ga bada lafiya

Duniyan Fasaha
Islah tasiu
+2349063541142
adsense match here
Share:

1 comment:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *