Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Illolin Kwalliyar Zamani Ga Fuskar Mace

Illolin Kwalliyar Zamani Ga Fuskar Mace

 

Assalamu Alaikum, Barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon Shirin namu na kwalliya wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha. 

Insha Allahu yau zamu maida hange ne a kan kwalliyar zamani da kuma yadda zai iya kasancewa matsala ga fatar mace. Wasu kwararrun masana kan kwalliya sun shawarci matan zamani akan rage yin kwalliya kullum domin yana iya bata musu ido da fuskoki haka zalika da wasu sassa na jiki.

Mata masu yawan son kwalliyar zamani basu san cewar; yawan chaba kwalliya na iya kawo matsalar rashin karfin ido da bata fuska ba.

Wasu matsaloli da kwalliyar zamani ke iya haifarwa sun hada da:

1=> Yana kawo cutar dajin fata, wato ‘Skin Cancer’

2=> Tsigewar gashi a jiki

3=> Yana tsufar da fata

4=> Yana rage karfin fata

5=> Rashin Daukar Ciki ga mace – A nan masana sun ce yawan irin wadannan shafe-shafe na iya sa mace ta gagara daukar ciki saboda akwai wasu abubuwa a cikin man da take shafawa da ke shiga ta ramukan gashi zuwa cikin jikin mace.

6=> Yawan ciwon kai.

7=> Yana kawo tsufa da wuri ga mace – Za kaga budurwa ta na tsofa haka kawai ba tare da dalili ba.

Masanan sun lissafo wasu hanyoyin da za’a iya bi domin samun kariya daga wadannan matsaloli da muka lissafa, hanyoyin sun hada da;

1=> A daina amfani da kayan kwalliyan da suka tsufa

2=> A rage yawan shafa jan hoda domin yawan shafa shi na kawo kurarraji a fuska haka zalika yana toshe ramukan iska na fuska.

3=> A daina amfani da ‘Contact Lense’ domin yana kawo makanta. Contact lense wani nau’in kwalliya ne da ya yi kama da leda wanda mata kan saka shi a ido domin cansa kalan idon su.

4=> A daina shafa tozalin zamani wanda wasu ke kira da ‘Gazar’ ko kuma da turanci ‘Eye Liner’ domin yana dauke da sinadarin dake kashe ido. Kamata ya yi a shafa tozalin gargajiya kokuma ‘Kajol’.

5=> Amfani da gashin idon kanti wato ‘Eye lashi’ a turance na kawo rashin karfin ido domin ana amfani da gam kafin a manna shi kan gashin ido wadda idan an je cirewa ya kan kawo wasu matsaloli kamar kumburin ido, rasa gashin ido, kurarraji da sauran su.

Waddannan sune wasu matsalolin da kwalliyar zamani ke haifarwa tare da wasu hanyoyi da za’a magance wayan nan matsalolin. Shin kina da wasu dabaru da za’a iya amfani dasu wajen magance wadannan matsalolin wadda bamu bayyano anan ba? 

Zaki iya rubuta mana a wajen akwatin ajiye sako dake kasa ko kuma ta hanyar tuntunanmu a layukan sadarwan mu da kuma hanyoyin sada zumuntanmu na facebook, twitter, Instagram da kuma telegram. Allah shi bamu ikon kiyayewa Ameen!.mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *