Mahimmancin Kankana Ga Lafiyar Jiki
Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka barkanmu
da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye
daga mujallar Duniyan Fasaha insha Allahu yau zamu tattaunane akan muhimmancin
kankana ga lafiyar jiki. Kankana kusan dukkanta ruwa ne don gwargwadon ruwan
dake cikinta masana sun qiyasta ya kai 90%-99% bisa dari, sukarin da ke cikinta
kuwa zai kai 8%, sannan ana samun vitamin C da vitamin B a cikinta, kamar yadda
ta tattara sinadarin Sulphur, Calories, Phosphor da kuma Potassium, wani
kuskure da wasu suke yi shi ne suna cire ‘ya’yan kankanan a lokacin da suke sha,
ba su san cewa kamata ya yi su tauna ba, ‘ya’yan ba su da daci sai dandanon mai
dadi ga Fat 43%, Sugar 16%, sai Protein 27.
==>
KODA: Kankana ta kan taimaka
wa koda matuka, domin ruwan da ke cikinta, kamar dai yadda aka sani takan
saukake wa taruwar fitsari da fitarsa, wannan saboda tana da sinadarin
Potassium wanda ya ke taimakawa wajen korar gurbataccen sinadari daga
jukkunammu, sannan sinadarin yana rage yawan sinadarin Hyperuricemia a cikin
jini.
==>
FATAR DAN ADAM: Dangane
da fatar dan adam, sananne ne cewa kankana tana da sinadarin da ya ke kare
jikin dan adam daga Oxidation, don haka ne ma take iya fatattakar tsattsakar
fata, da lalacewarta, takan ba wa fata kariya daga hasken rana mai cutarwa,
masamman yadda take dauke da sinadarin Lycopene da Crotin wadanda suke
taimakawa wajen kare jikin dan adam daga kunar ranar da take sanya cutar fata
ko kuma cancer wace take samun fatar.
==>
HAWAN JINI: Sai kuma
mutane masu fama da mummunar bugawar jini, kankana takan taimaka musu saboda
tana kunshe da sinadarai kamar su Manganese da Potassium masu aiki wajen tsara bugawar
jinin, matuqar kankana ta qumshi wadannan sinadaran kenan ta dace da mutum mai
fama da hawan jini ya riqe ta a matsayin qari cikin abincin da yake iya ci a
kullum.
==>
CIWON SUGAR: Kamar dai
yadda muka fadi ne a baya cewa kankana ta qumshi sinadarin Potassium da Magnesium
wadanda aikinsu shi ne taimaka wa jiki wajen tatso sinadarin Insulin wanda yake
tsara wa sukari yadda zai yi aiki a cikin jini, qarancin wannan sinadari shi
yake hana iya sarrafa sinadarin Glucose da mutum ya samu a jikinsa ta hanyar wasu
abinci masu masifar zaqi, ko wurin wasu ‘ya’yayen bishiyar, a nan cin kankanan
zai taimaka wa mai cutar ko ta ba wa wanda bai da ita wata kariya.
==>
KUZARIN JIKI: Ana aiki
da kankana a matsayin wata madogara ta dabi’a wace take maye makwafin wasu magunguna
masu kara wa mutum kuzari a jiki da qarfi da lafiya, wadanda galibin ‘yan wasan
motsa jiki su suke amfani da su, domin kankana tana da dauke da Potassium da
Magnesium da kuma Vitamin B da nau’o’insa wanda shi kuma yake qara kuzarin
jiki.
==>
MATSALOLIN IDO: Kankana
takan taimaka wa ido wajen kare ganin mutum, don tana dauke da Vitamin A wanda yake
da mahimci ga idon mutum, wani bincike ya gano cewa in dai mutum zai sanya
kankana a gaba kullum zai ci na kimanin yankar N100 a yau, to ba ko shakka
kankana za ta taimaka masa wajen kyautata ganinsa masamman domin wadan da
ganinsu yake raguwa a dalilin aiki da na’urorin zamani kamar su talabijin,
wayoyi da kwafyuta, ko kuma don tsufa.
No comments:
Post a Comment