Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda za a samu fata mai haske

Yadda za a samu fata mai haske

Yadda za a samu fata mai haske

Mata da dama na sha’awar samun fata mai haske kuma mai sheki. Gaskiyar magana ita ce, ba zai yiwu mace ta dada haske a cikin kwana daya ba. Amma akwai abubuwan da za ta yi domin samun irin wannan launin fatar da take so. Don haka ne a yau na kawo muku irin abubuwan da za a yi domin samun fata mai haske kuma mai sheki daga dakin girkin uwargida ba sai an je kasuwa ko manyan shagunan sayar da kayan kwalliya ba.

==> Kurkum: yana dauke da sinadaran haskaka fata da kuma warkar da tabon fuska. Yana da kyau a kasance tare da shi. A samo zuma cokali biyu sannan a kwaba da garin kurkum sannan a rika shafawa a fuska na tsawon mintuna talatin a kullum kafin a shiga wanka. Yana dada wa fatar jiki haske.


==> Timatur: yana dauke da sinadarin ‘lycopene’ wanda ke taimakawa wajen haskaka fata. Idan har ana so a dada haske a sati daya, sai a markada timatur sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki sannan a shafa a fuska da wuya a kullum na tsawon mintuna 20 kafin a wanke.

==> Ruwan ‘rose’: idan ana son amfani da wannan hanyar don dada hasken fuska, sai a rika diga shi a cikin man shafawa, yana sanya fata laushi da kuma haske. Ko kuma a samu garin alkama sannan a kwaba da ruwan ‘rose’ sannan a shafa a fuska da wuya na tsawon mintuna 20 kafin a wanke.


==> Zuma da lemun tsami: wadannan ababen na saurin sanya fata yin haske da kuma sheki. A samu zuma da lemun tsami sannan a kwaba su a rika shafawa a fatar fuska da jiki sannan a barshi na tsawon mintuna 30 sannan a wanke kamar sau biyu a rana safe da yamma.
==> Kurkum da madara: a kwaba garin kurkum da madara sannan a shafa a fuska a kwana da shi. Washegari a wanke. Yana sanya fuska haske da kuma sheki.

==> Fiya da gurji: a markada fiya da gurji sannan a rika shafawa a fuska na tsawon mintuna 30 a kullum kafin a wanke. Yana sanya haske da kuma shekin fata.

Masu karatu su gane cewa a cikin ababen da na lissafo, guda daya yakamata mutum ya yi amfani da shi domin samun sakamako mai kyau. Amfani da su duka a lokaci daya na haifar da kurajen fuska.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive