Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda za’a Magance Kyasbi ciin sauki

Yadda za’a Magance Kyasbi ciin sauki

Yadda za’a Magance Kyasbi ciin sauki

Assalamu Alikum Barkaku da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu dake kawo muku daga zaurennan na Duniyar Fasaha Insha Allahu yau zamuyi bayanine akan wannan babbar cutar wato kyasbi, kyasbi mummunar cuta ne da ke addabar fata. Babban abin damuwar shi ne bai cika warkewa da wuri ba. Abubuwa da dama na sanya mutum ya kamu da kyasbi. Kamar kyankyani ko damina. Idan mutum na da fata mai gautsi, hakan na kawo kyasbi. Yadda mutum zai gane cewa ya kamu da kyasbi kuwa shi ne, zai rika yawan jin kaikayi a fatarsa. Kuma idan ya sosa wurin sai ya ga kuraje sun feso masa. Za a iya samun kyasbi a iyalin da suke da tarihin ciwon asma (Asthma). Har yanzu ba a samu maganin da ke warkar da kyasbi ba amma akwai hanyoyi da dama wanda za a iya amfani da su don samun sauki.


Hanyoyin magance kyasbi Mayuka da dama na magance kyasbi, misali man kwakwa da zaitun da kuma na aloe bera. Man kwakwa na dauke da sinadarin ‘fatty’ da ‘luric acid’ wadanda suke taimaka wa fata wajen magance duk cututtukan fata. Man kwakwa da na zaitun na da amfani sosai ga fatarmu, musamman ma wajen magance kyasbi. Idan mutum yana da kyasbi, ya kamata ya daina barin jikinsa a bushe. Za a iya shafa man zaitun ko man kwakwa a wurin da kyasbin ya feso. Ko kuma a samu ruwan aloe bera ana shafawa a kan kyasbin. Za a iya hada sakar zuma da man zaitun da man kwakwa da kuma na aloe bera a wuri daya. Sai a kwaba hadin har sai ya gaurayu da kyau kafin a shafa a kan kyasbi. Idan an shafa, sai a jira na tsawon awa daya kafin a wanke. Muna son masu karatu su yi hakuri da irin wannan maganin, saboda duk abin da ya shafi fata, yakan dauki lokaci kafin ya warke.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive