Wannan lamari na barin account da
mutumin da ya rasu a social
network yana baiwa mutane da dama haushi da takaici, musamman
waɗanda suke kusa da wanda ya mutu. A wani lokaci za ka ga mutane suna jingina
(tagging)
hotunan banza ko na batsa ga shi wannan mamaci, haka za ka samu duk shekara
mutane su yi ta mai murnar cika shekara (birthday)
amma alhali shi yana lahira, wasu waɗanda suka saba wasa da shi, idan suka yi
magana da shi bai amsa ba su yi fushi ko zagi da dai makamantan su.
Muna yawan samun ƙorafe-ƙorafe a wurin jama’a musamman waɗanda
suka damu da makomar ‘yan uwansu waɗanda suke da account a Facebook ko Twitter ga shi kuma
Allah Ya yi musu mutuwa dangane da ya za ayi su iya goge wannan account domin yadda
hankalinsu yake tashi duk lokacin da suka ga hotonshi ko kuma wani abu
makamanci haka.
Wannan dalilin ne ya sa muka yi bincike muka gano ashe tun
tsawon wancan lokacin da muke ganin haka tuni kamfanin Facebook suka fito
da wani fom wanda shi ne kawai abin da kake buƙata domin goge irin wannan account ɗin.
A GYARA HALI KAFIN A MUTU.
Yana da kyau duk wanda yake karanta wannan takarda ya sani wata
rana shi ne wanda mutuwa zata riske shi, kuma bai san wani lokaci ba ne, kuma
bai san a wani hali ba ne. Yana da kyau mu riƙa tsaftace abubuwan da muke
sakawa social networks
domin duk abin da ka saka yana nan kuma wani ya killace shi. Kuma dani da ku
duk mun san watan wata rana za a tambaye mu, kuma sai mun bayar da bahasi a
kai.
Mutane da dama basa la’akari da cewar duk abin da na rubuta ko
na saka a social
network Allah zai tambaye ni, idan na saka wata magana ta karya
wani ya yaɗa to zunubin yana kaina, haka idan na yaɗa abin da yake na alkairi
ladan yana kaina. Mu guji yiwa mutane ƙazafi, saka hotunan da basu dace ba, da
kuma yaɗa jita-jita da zarge-zarge domin waɗannan abubuwan suna da wahalar tuba
kuma suna da wahalar kankarewa.
INA ZAN SAMI FOM DA ZAN CIKE
Shi wannan fom da za ka cike, yana da waɗansu ƙa’idodi da ya
kamata mutum ya sani, kuma akwai abu mai muhimmanci da koya ya kamata ya
kiyaye.
Kamfanin Facebook basa
la’akari da garinka ko kuma addinin ka, suna la’akari da addininsu da kuma
al’adunsu, saboda haka abin da suke buƙata wurin cike fom ɗin shi ne takardar
shaidar cewar wannan mutumin ya mutu wacce kotu ko Asibiti suke bayarwa. Saboda
haka kafin ka fara cike wannan fom sai ka je ka karɓi takardar shaidar cewar
wane ya mutu, sannan kayi scanning sai
ka fara cike fom ɗin.
Za a iya buɗe wannan fom ɗin
ta bin wannan link kamar haka https://www.Facebook.com/help/contact/228813257197480
Fom ɗin wanda da Turanci aka rubuta shi yana buƙatar ka amsa
tambayoyi guda takwas (8) kafin ka aika shi wanda su kamfanin Facebook za su duba
su gani sannan daga baya su goge shi wannan account ɗin.
TAMBAYOYI DA AKA AMSA
1. Cikakken Suna: A wannan ɓangare
ana son kai da za ka cike wannan fom ɗin ka saka sunanka cikakke misalin Muhammad Hassan
2. Sunan wanda ya mutu: shi kuma
rami na biyu sai ka rubuta cikakken sunan wanda kake son a goge account ɗinshi,
namiji ne ko mace.
3. Email ɗin mamaci: a na son
ka saka imel ɗin da kake tunanin cewar da shi wannan mamacin ya buɗe account, kodayake wannan
email ba dole ne ka san shi ba, kuma idan ma baka cike wannan ramin ba saboda
rashin sani babu matsala, amma saka email ɗin zai baiwa kamfanin sauƙi zaƙulo account ɗin kuma su
goge shi.
4. Link ɗin mamaci na Facebook: duk
mutumin da ya buɗe Facebook,
suna bashi wani link (hanya
ko rariyar liƙau) da ita ce hanyar shiga shafin ka kai tsaye, kuma wannan hanya
babu mai ita a Facebook sai
kai. Misali nawa shine https://Facebook.com/muhammadabbaganakolo duk mutumin da ya rubuta wannan link a jikin browser to zai
kaishi shafi na na Facebook kai
tsaye. To idan baka san na wanda ya mutu ba, abin da za ka yi shi ne ka nemo
shi a cikin abokanenka, sai ka taɓa sunan shi, zai kai ka kai tsaye cikin
shafin sa, sai kayi amfani da browser ka
kwafe link ɗin
da ka gani sai ka saka a wannan ramin.
5. Dangantar ka da mamaci:
lallai Facebook suna
buƙatar su san dangantakar da wannan mamaci kafin su cire wannan shafi a
gidansu. Saboda haka za ka zaɓi dangantakar ka, a cikin kashi uku da suke da
shi.
1. Iyalai mafi kusa: kai ɗan
uwansa ne, ko baban sa, ko matar sa ko kuma yayan sa da dai makamanta su.
2. Dangantakar jini: kamar
kaka, goggo, baffa, da kawu da dai makusanta na jini
3. Abokantaka: idan wanda
ya rasu, abokinsa ne ko kuna aiki wuri guda ne ko kuma aji ɗaya kuka yi, ko
kuma ma dai ka san cewar ya mutu ne, sai ka zaɓi nan.
6. Me kake son Facebook su yi da account ɗin: a nan Facebook suna
son ka faɗa musu abin da kake son ayi maka da account ɗin domin ba goge shi kaɗai za
su iya yi ba, a nan akwai abu guda hudu (4) da za ka iya basu dama su yi.
1. A faɗawa abokansa ya mutu:
wannan zabi ne da za ka ba Facebook na
su saka a cikin shafin sa cewar wane fa yanzu ba shi, ya mutu, kuma su saka
alamar da kowa zai iya ganewa cewar yanzu da gaske babu shi.
2. A goge account ɗin sa: wannan shi
ne ɓangaren da ya fi kyau ayi amfani da shi, domin zai ba Facebook dama su
share dukkan abin da wannan mamacin ya saka a cikin Facebook, tun daga
rubutunsa, likes da comments da sharing da hotuna
da video da yasa a Facebook,
yadda ba shi suna ba su.
3. Ina da buƙata ta musamman:
idan kuwa akwai wani abu da kake buƙatar Facebook su yi maka ba sharewa ba to
sai ka zaɓi wannan ɓangare.
4. Ina da tambaya: wannan
kuma idan kana da tambaya da kake son kayi wa Facebook sai ka zaɓi wannan ɓangare.
7. Yaushe mamacin ya rasu?: a
wannan ɓangare suna son ka zaɓi rana da wata da shekarar da ya mutu ka saka
musu.
8. Takardar shaidai mutuwarsa: a wannan wurin shi ne za ka sakawa Facebooktakardar shaida
daga kotu ko asibitin da mutum ya mutu cewar wannan mutumin ya mutu, ko shaida
da mutane gidansu cewar su suka baka izini cewar Facebook su cire
shafinsa.
9. Da zarar ka gama cikewa sai ka aika musu da wannan fom domin su
duba su gani sannan su yi abin da ka ce kana so.
Ba kamar yadda mutane suka tsammani ba, zai ɗan ɗauki lokaci
kafin kamfanin Facebook
su waiwayi takardar, domin kamfanin da yake da mutane sama da
biliyan daya da rabi yana buƙatar lokaci kafin ya aiwatar da wani abu. Kai dai
tunda ka aiki sai ka jira.
Kuma babu laifi idan mutane mabanbanta suka aika, misali a sami
mutane da yawa su aika domin hakan zai sa Facebook su gane cewar wannan bawan
Allah da gaske ne cewar ya mutu.
Muna rokon Allah Ya jiƙan waɗanda suka riga mu mutuwa da imani,
Ya kyautata ƙarshenmu ya yafe mana kurakuranmu, ya amintar da mu baki ɗaya.
Amin
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Shin mutum Yana iya delete din Facebook account din shi kuwa? Misali in banason in cigaba da amfani da Facebook din, Yaya zan yi?
ReplyDeleteKwarai ma kuwa
Delete