Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Soyayyen dankali da nama da kabeji

Soyayyen dankali da nama da kabeji

Soyayyen dankali da nama da kabeji
Assalamu alaikum Uwargida. Yaya sanyi? Allah Ya fiddamu lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka soyayyen dankalin turawa da nama da kabeji domin samun abun karyawa. Akwai ababe da dama wadanda za’a iya karyawa dasu. Yana da kyau a rika sauya girki daban-daban domin kada ya ginshi mutanen gidan. Shi dai wannan girkin ba daurasu akan wuta gaba daya ake ba. Daban ake yinsu sannan a sanyasu a wuri daya domin su kara dadi a lokacin karyawa.


Abubuwan da ake bukata

·        Dankalin turawa
·        Nama
·        kwai
·        Tumatir
·        Kabeji
·        Bama
·        Magi
·        Garin tafarnuwa
·        Man gyada
Hadi

A samu dankalin turawa sannan a fere shi ba tare da daddatsa shi ba sannan a wanke a ajiye a gefe. A tafasa dankalin da ruwa da gishiri kadan sannan a tsame. A fasa kwai kamar uku sannan a zuba magi da yankakkiyar albasa kanana sosai da garin kori da na tafarnuwa domin cire karnin kwan. A daura tukunya a zuba man gyada har sai tayi zafi sannan a dauko dankali ana tsomawa a kwai ana jefawa a mangyada. Haka za a rika yi har sai sun soyu. Sannan a kwashe a zuba a rufe a kwano mai murfi.

 A tafasa nama da magi da gishiri da garin tafarnuwa da na kori sannan a yayyanka mishi albasa har sai yayi laushi sosai ruwan ya kusa tsotsewa sannan a sake yayyanka albasa da timatir a zuba da man gyada kadan ayi ta gaurayawa akan wuta har sai albasar da timatir din sun nuna. Sai a kwashe a ajiye a gefe. A samu kabeji a yayyanka shi kanana sannan a tafasa kwai kamar uku a yayyanka da dan girma a ciki sannan a sami bama da magi kadan a zuba a gauraya. A samu kwano a zuba soyayyen dankalin a gefe, hadin nama a wani gefen sannan hadin kabeji a wani gefen. Za’a iya hada wannan kayan karyawan da bakin shayi ko kuma mai kauri. A ci dadi lafiya!


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive