Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Hanyoyi biyar da ke haifar da gautsin fata

Hanyoyi biyar da ke haifar da gautsin fata

Hanyoyi biyar da ke haifar da gautsin fata

Assalamu Alaikum matan gidan nan. Yaya sanyi da yara, tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Akwai abubuwa da dama da sanyi ke janyo wa fata, kamar gautsin fata da sauransu. Don haka ne a yau na kawo muku yadda wadannan al’amura ke faruwa da kuma yadda za a magance su.

A sani cewa fata ita ce mace, in ta yi kyau za ta rika haskawa a lokacin tashen shekar unta; in kuwa ta baci lallai tsufan mace zai bayyana da wuri, ko da ba ta kai shekarun ba. A sha karatu lafiya.

Rashin shan isashen ruwa; ruwa na da matukar mahimmanci a fata. Don haka ya kamata a dage da shan ruwa da kuma cin kayan lambu da kuma ’ya’yan itatuwa. Rashin shan ruwa na haifar da gautsin fata.


Am fani da sabulu mai zafi; yawan amfani da sabulan dake dauke da sinadarai masu karfi na illatar da fata da kuma haifar da samun gautsi a fata. Don haka sai a kula. A samu sabulu wanda ba su dauke da sinadaren illatar da fata kamar su sabulan yara da sauransu.

kura; yana karya sinadarin bitamin A a jiki wanda ke da mahimmanci wajen gyaran mataccen fata. A rage bude fatar jiki a wajen da ke da kura. Domin ba iskar gari kawai ke kawo shi ba, shan taba sigari ko kuma zama a inda ake sha zai iya zama matsala ga lafiyar fata.

Shafe-shafe; yawan amfani da kayan shafe-shafe da ake yinsu da sinadaran maiko na shanye maikon da ke cikin fata, kuma hakan yakan haifar da yamutsewar fata.

Amfani da mayuka masu dauke da turaruka masu karfi; matsalar dake tattare da amfani da irin wadannan mayuka shi ne, yawwan shafa ta a lokuta da dama, yin hakan na sanya sinadarin da ke gyara fata ya daina amfani a jikin mutum.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive