Assalamu Alaikum insha Allahu yau zamuyi bayanine dangane da yadda ake amfani da madara wajen magance maikon fuska, hakika Shan madara na kara lafiyar jiki sosai, tana sanya fata ta rika sheki, tana kuma sanya ta ta yi taushi da kuma santsi. Hakan ya sa a yau Duniyan Fasaha ta kawo muku yadda ya kamata ku yi amfani da madara wajen magance yawan maikon fuska.
Abubuwan bukata
Madara
Gishiri
Ruwa
Auduga
Zuma
Amfanin madara wajen magance maikon fuska
Hakika Madara na goge daudar fuska: A samu madara rabin kofi, sannan a hada ta da rabin cokalin gishiri, sai a sanya ruwa a gauraya har sai gishirin ya narke. Daga nan sai a shafa a fuska da wuya zuwa minti 2 ko 3 kafin a wanke da ruwan dumi.
Madara na sanya fata santsi: don haka za a iya amfani da ita a matsayin sinadarin ‘cleanser’. Da farko a samu auduga, sai a tsoma a cikin madarar ruwa, daga nan a rika goge fuska da ita. Daga nan a jira ta bushe ka_n a wanke. Yin hakan na rage maikon fuska, kuma zai sanya fuska ta yi taushi da santsi.
Za a iya amfani da madara don kara wa gashi karfi: musamman lokacin sanyi da gashi yakan tsinke. A zuba madara a kan gashi a cuda har ta taba tsagun kai, sai a jira na minti kadan kafin a wanke. Yin hakan na kara karfin gashi kuma yana hana shi tsinkewa.
Za a iya hada madara da zuma sannan a shafa a fuska. Yin haka na hana tsagewar fatar fuska saboda sanyi.
No comments:
Post a Comment