Sau da yawa mutane sukan yi kukan kiba ta yi musu yawa, har suna shiga wani hali a sakamakon hakan. Idan wannan ne matsalar, sai na ce a kwantar da hankali, domin a wannan makon na taho muku da hanyoyin da za’a bi wajen rage kiba. Ga bayanin hanyoyin da za’a bi kamar haka:
=> A riga cin ganyayyaki da suka hada da alayyahu da salak da zogale da sauransu, domin suna dauke da sinadaran da ba sa sanya kiba, suna matukar taimakawa wajen gyara jiki.
=> Ya kamata a ringa cin ‘ya’yan itatuwa da suka hada da lemo da ayaba da abarba da mangwaro da kankana da kwakwa da sauransu, domin irin wadannan ‘ya’yan itatuwa suna tsotse sinadaran da suke sanya kiba, sannan su rage kibar jiki.
=>Ana so a guji cin duk wani abincin da yake da gishiri mai yawa, kasancewar masana kiwon lafiya sun yi bincike, sun kuma gano samuwar gishiri da yawa a jiki yana jawo kiba.
=> Yana da kyau a guji yawan shan madara, ko yawan amfani da ‘butter’, wadannan nau’ikan kayan abincin suna dauke da sinadaran da suke sanya kiba. Haka ya kamata a guji cin nama mai kitse da yawa, domin hakan zai sanya mutum yayi kiba.
=> A ringa amfani da citta da kanamfari da masaro, wani lokaci kuma da barkwano, domin suna dauke da sinadaran da ke rage kiba.
=> A ringa shan madaci da duma mai daci, domin suna dauke da sinadaran da ke rage kiba.
=> Shan zuma wata hanya ne da za’a bi idan ana son rage kiba. Zuma na taimakawa wajen taso da sinadaran da suke sanya kiba, wadanda ke kwance a cikin jiki, tana fito da su ne don su bi jiki a lokacin da mutum yake aikin karfi, raguwarsu a jiki zai sanya ki rage kiba. A lokacin da za’a sha zumar ya kamata a gauraya zumar da ruwan zafi, sannan ana so idan har za’a sha zumar, to a sha da sanyin safiya, idan an tashi sallar asuba ko kuma lokacin da aka farka daga barci. Kuma idan aka gauraya zuma da ruwan zafi da kuma lemon tsami, sannan aka sha za su taimaka wajen rage kiba.
=> A ringa yawaita cin kabeji, kasancewar kabeji yana taimakawa wajen rage kiba. Kabeji yana taimakawa wajen rage yawan sinadaran da suke sanya kiba. Za’a iya cin kabejin danyensa ko kuma bayan an dafa.
=> Motsa jiki yana taimakawa wajen rage kiba. Motsa jikin da ake yi yana taimakawa wajen kone sinadaran da suke sanya kiba. Haka kuma yana sanya jijiyoyin jiki su sake. A lokacin da za’a fara motsa jiki ya kamata a fara daga tafiya, daga nan sai a fara gudu kadan-kadan, sannan za’a iya iyo a cikin ruwa idan kuna da wajen wanka na zamani.
=> Shan lemon tsami ko ruwan jus din lemon tsami na rage kiba. Za’z iya gauraya jus din lemon tsami da ruwa mai dumi da kuma zuma, sannan a ringa sha duk safiya, hakan zai taimaka sosai wajen rage kiba.
=> A guji yawan cin abinci, domin hakan yana sanya mutum kiba sosai.
No comments:
Post a Comment