Mene ne Programing Language?
WANI TSARARREN RUBUTU NE DA AKE YI DOMIN KURMAN MASHIN, AMMA KUMA YA
SANYA SHI YA KASANCE MAI JI KAMAR MAI KUNNE.
Daga
ina ya kamata ka fara?
Mene
ne dalilin da ya sa ka ke son ka fara yin Programing Language ? Wannan ita tambayar
da ya kamata ka fara yi wa kanka da kanka, kasancewar kowane Programing Language akwai
abin da ya ke yi, da kuma abin da ake iya yi da shi, da kuma irin mashin ɗin da
ya ke iya sarrafawa, da kuma alaƙar da take tsakanin sa da sauran Programing Language da
ake da su.
Programing Language nawa ne a duniya?
Programing
Language suna da matuƙar
yawa, tun daga wanda ake amfani da shi a cikin ƙananan na’urori da kuma manya,
da waɗanda ake amfani da su a cikin gida da kuma ma’aikatu da kuma waɗanda ake
amfani da su a harkokin mu na yau da kullum. Sai dai a cikin waɗannan Programing Language ɗin
akwai waɗanda suka sami karɓuwa akwai waɗanda ko sunan su ma ba mutane da yawa
ba su san su ba.
A
wannan muƙalar zamu ɗauki yaren Kwamfuta waɗanda su ka fi shahara guda tara (9)
a wannan zamani, waɗanda kuma da su ne duniya ke taƙama kuma kusan duk wani abu
da za ka gani a wannan lokaci idan dai na’ura ce, tun daga kayan wasan yara (games) da na’urorin da manya
suke amfani da su kamar wayoyin tafi-da-gidanka, da ma manya da ƙananan
manhajoji dukkaninsu ba sa wuce ɗaya daga cikin waɗannan Programing Language ɗin.
Wadannan
programming guda tara ne, waɗanda suka hada da
·
Python
·
JAVA
·
C
·
PHP
·
C++
·
JavaScript
·
C#
·
Ruby
·
Objective-C
Mene
ne dalilin ya zai sa na koyi Programing
Language ?
Akwai
ra’ayin mabambanta ga masu koyon yaran kwamfuta. Waɗannan dalilai sun sha
bambam, sai dai daga baya ra’ayin yana komawa ga mataki na karshe amma kuma
dukkansu babu matsala ga wanda mutum ya ɗauka.
An
tattara ra’ayoyin jama’a masu koyon Computer
Programming har gida shida (6), ta hayar la’akari da ta ina
mutum ya ɓullo da kuma ina yake son ya ɓulla a wannan harkar.
·
Ba su san dalilin da ya sa suke koyon programming
·
Domin amfani yara.
·
Domin jin daɗi da nishadantar wa
·
Yana da ra’ayin yin programming
·
Yana son ƙarawa kanshi sani a cikin Programing Language
·
Domin ya sami kudi.
A
darasin mu na gaba za mu ɗauki kowane ɗaya daga cikin waɗannan ra’ayoyi mu bada
shawara ingantacciya ga duk mutumin da yake son ya koyi programmig language
cikin wadannan ra’ayoyi shida.
In
Sha Allah.
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
No comments:
Post a Comment