Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda ake yin mashe- Girke Girke


Yadda ake yin mashe- Girke Girke

Assalamu Alaikum Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau mun kawo muku yadda ake yin mashe. Mashe abinci ne mai kama da masa amma ya fi masar kankanta sannan abubuwan da ake amfani da su wajen sarrafa shi daban yake da na masa ko waina. An fi cin wannan irin abincin ne a kasar Hausawa domin karyawa da safe. Sannan mafi yawanci sun fi son cin sa da yajin kuli-kuli ko kuma yajin barkono. A sha karatu lafiya.

Abubuwan da ake bukata


Ø  Garin gero
Ø  Man gyada
Ø  Magi
Ø  Yis
Ø  Flawa
Ø  Gishiri
Ø  kuli/yaji

Hadi

A samu gero sannan a wanke a cire tsakuwa a busar sannan a kai a nika ba tare da an saka kayan kamshi ba ko kayan yaji. Bayan haka, sai a tankade wannan garin sannan a sa a roba sai a samu garin flawa a zuba a ciki a gauraya su gaurayu sosai. A duma ruwa sannan a zuba yis a ciki idan ya dan tashi, sai a zuba a cikin hadin garin gero da flawa. A samu ruwa ana zubawa ana kwaba hadin har sai ya yi kauri kadan. Hadin ya kasance ba mai kauri sosai ba sannan a rufe a sanya a rana har sai kullun ya tashi.

Sannan a dora tukunyar tuya a wuta a zuba man gyada da albasa su soyu. Sai a dauko kullun ana yankawa da ludayi ko cokali daidai girman da ake so ana soyawa kamar yadda ake tuyar fanke sannan a kwashe. A samu yajin kuli mai dauke da magi a ci da shi ko kuma yaji mai dauke da magi ana dangwalawa ana ci.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive