Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Hanyoyin Da Ake Gano Zumar Da Aka Yi Wa Algus

Hanyoyin Da Ake Gano Zumar Da Aka Yi Wa Algus

Hanyoyin Da Ake Gano Zumar Da Aka Yi Wa Algus


Assalamu Alaikum Barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu insha Allahu yau zamu tattauna akan hanyoyin da ake gano zumar da akayi wa Algus, ma’ana zumar da aka sauya masa yanayi, Mutane da dama su kan ji tsoron sayen zuma saboda ba sa iya banbance tsakanin  mai kyau da wacce aka yi wa algus. A hakikanin gaskiya Akwai hanyoyi daban daban masu sauki da ake amfani da su wajen gane zumar da aka gurbata  amma yau zan tattauna manyan da akafi ganewa cikin sauki suna nan kamar haka:

=> Gwajin ruwa: Zuma mai kyau ba ta narkewa da zaran an zuba ta a cikin ruwa, za ta tafi kasan ruwan ne ta kwanta yayin da mai algus da zaran an zuba ta a ruwa za ta gauraye da ruwan.

=> Gwajin Ashana: Idan aka dangwala ashana a cikin zuma mai kyau aka kyasta ta za ta kunnu ba tare da matsala ba yayin da zuma mai algus za ta hana ashanar kunnuwa.


=> Kwajin Biredi: Idan aka shafa zuma mai kyau akan biredi, biredin ba ya laushi sai dai ya kara tauri, yayin da biredin zai nadi zumar kamar yadda yake nadar ruwa sannan ya yi laushi idan ba mai kyau ba ce.

=> Gwajin Kwanduwa: Idan aka zuba zuma mai kyau akan kwanduwar da aka _tar da ita daga cikin danyen kwai aka gauraye su tare, za a ga kwanduwar ta koma kamar an dafa. Zuma mai algus kuwa ba ta da wani tasiri akan kwanduwa.

Baya ga wadannan hanyoyi hudu, mutum zai iya gano zuma mai kyau daga dandano da kamshin ta. Zuma ba ta daci daci ko kauri a baki sai dai idan an hada ta da narkakkiyar suga.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive