Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Hanyoyi 5 da za ki magance zubewar gashin kai


Sau da dama mata kan samu kansu cikin shiga ukun zubewar gashi, wanda yawancin hakan na faruwa ne a garin neman a gyara gashin kai, sai kuma a bata, karshe gashin kai ya zube. Don haka ne na taho miki da hanyoyi biyar da idan kin bi kowacce daga ciki za ta magance miki zubewar gashin kanki, ta kuma kara wa gashin kanki tsawo da kyawu da kuma sheki.

    1.     Amfani da mayukan gashin kai: Ki samu daya daga cikin man gashin kai kamar su, Man Olibe oil da Coconut oil da Canola oil da sauransu. Daga nan sai ki zuba daya daga cikin man da na lissafa a sama a cikin tukunya, sannan ki dora a kan wuta. Ki bar shi ya yi zafi, amma ba wai sosai ko ya tafasa ba. Bayan nan sai ki sauke daga kan wuta, sannan ki shafa a gashin kanki. Yana da kyau ki shafa a kofofin gashin kanki, hakan zai taimaka wajen sanya gashin kanki ya yi tsawo da kuma sheki. Idan kin shafa sai ki rika amfani da hannuwanki wajen goggogawa da dan karfi-karfi. Bayan nan sai ki sanya hular ‘shower cap’ har zuwa awa daya. Bayan nan sai ki shafa man shampoo. Daga nan sai ki wanke kanki.

   2.     Amfanin da jus din citta ko tafarnuwa ko albasa: Ki samu albasa ko citta ko tafarnuwa, sannan ki markada daya daga cikinsu har ta zama kamar jus. Daga nan sai ki shafa a gashin kanki. Yana da kyau idan kika shafa sai ki kwana da shi. Da safe sai ki wanke sosai. Yin hakan zai magance miki zubewar gashin kai.

    3.     Tausa a kai da kuma gashin kai: Idan kina tausar gashin kanki lokaci zuwa lokaci yakan haifar da gudanar jini cikin sauki a kofofin gashin kanki. Masana kiwon lafiya sun ce idan har jini na gudana yadda ya kamata a kofofin gashin kai, to hakan zai sanya gashin kai ya kara tsawo. Shafa man essential oil kamar su Labender da bay essential oil da almond da kuma sesame a lokacin da za a yi tausar kai ko gashin kai yana sanya gashin kai ya kara tsawo da kyau da kuma sheki.

    4.     Amfani da abin da yake kashe kwayoyin cuta: Idan kina shafa abin da yake kasha kwayoyin cuta a gashin kanki zai hana gashin kanki zubewa. Misali ki samu kwalin ko ledar ganyen shayin ‘Green tea’ biyu, sai ki jika su a cikin kofi daya da ruwan zafi. Bayan ya huce, sai ki shafa a gashin kanki. Idan kin yi hakan za ki bar shi har zuwa awa daya, daga nan sai ki wanke. Ganyen shayin green tea yana dauke da sinadaran da ke hana zubewar gashi, a lokaci guda yana kara yawan gashin kai.

    5.     Ki rika samun hutu: Masana kiwon lafiya sun tabbatar da aikin wuya, rashin kwanciyar hankali hade da gajiya na haifar da zubewar gashi. Don haka idan ba kya so gashin kanki ya zube sai ki rika hutawa, a lokaci guda ki gujewa aikin wahala.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *