Kula da gashi
Gashi kamar sauran bangarori na jikin dan
Adam shi ma yana bukatar kulawa kwarai da gaske. Idan ya kasance gashi ba ya
smaun kulawar da ta kamata to babu shakka zai kararraye ya kuma kade saboda
iska ko rashin cikkakkiyar kula. Ga wasu hanyoyi da ya kamata mace ta bi wajen
kula da gashinta.
==>
Idan za a wanke gashi a yi mishi abin da ake kira steaming. Wata hanya ce ta wanke gashi bayan an shafe
gashin da hadin manshanu ko kuma na kanti sai a sami hular leda ko kuma ledar a
rufe gashin da ita. Bayan ya dauki kamar mintuna 30 sai a sa sabulu a wanke
gashin tas da ruwan zafi da kuma sabulun wankin gashi mai kyau.
==> Ya kasance da zarar gashin ya bushe a shafe
shi da mai sosai. Ma’ana abi gashin layilayi a rika shafa masa mai (Abin da ake
kira da turanci oiling).
==>
Akwai bukatar a rika kitso akaiakai saboda
yawan tazar gashin shi ma hanya ce da ke sanya gashi kadewa.
==>
A rika shafawa kitson mai (wanda ake amfani
da shi don gashi) a kullum saboda ana bukatar kullum gashin ya kasance cikin
danshi kada ya ya zama a bushe.
==> A kula cewa a lokacin hunturu man gashi mai
ruwa wanda ake kira oil shi ya fi kyau ga gashi.
==> A rage yawan sanya wa gashi man shamfo
(relader). A rika bari yana daukar tsawon watanni kafin akai ga yin shamfo. Idan
ya kasance gashinki mai tauri ne ki yawaita yin sitimin a maimakon shampoo.
No comments:
Post a Comment